Oliseh ya gayyaci dan kwallon Liberpool don ya yi wa Najeriya kwallo

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh ya fara yunkurin tuntubar matashin dan kwallon Liberpool da ke Ingila Jordan Ibe don ya yi wa Najeriya kwallo.Kafar watsa labaran wasanni ta africanfootball.com ta ruwaito cewa kocin yana kokarin ganawa da dan kwallon a Landon ne don shawo kansa ya buga wa Najeriya kwallo […]

Oliseh ya gayyaci dan kwallon Liberpool don ya yi wa Najeriya kwallo
Oliseh ya gayyaci dan kwallon Liberpool don ya yi wa Najeriya kwallo

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh ya fara yunkurin tuntubar matashin dan kwallon Liberpool da ke Ingila Jordan Ibe don ya yi wa Najeriya kwallo.
Kafar watsa labaran wasanni ta africanfootball.com ta ruwaito cewa kocin yana kokarin ganawa da dan kwallon a Landon ne don shawo kansa ya buga wa Najeriya kwallo a matakin manya.
Shi dai matashin dan kwallon. mahaifinsa dan Najeriya ne yayin da mahaifiyarsa kuma haifaffiyar Ingila ce da hakan ya sa yake da ruwa biyu, kuma yana da zabin kasar da zai yi wa wasa.
Kodayake dan kwallon, mai kimanin shekara 19 ya taba buga wa Ingila wasanni a matakin kungiyoyin kwallon kafa na matasa duk da haka zai iya yi wa Najeriya kwallo a matakin manya tun da bai taba yi wa babbar kungiyar kwallon kafa ta Ingila wasa ba, kamar yadda dokar hukumar kwallon kafa ta FIFA ta nuna.
Oliseh wanda ya sanya hannu a kwantaragin shekaru uku a makon jiya, tuni ya koma Turai don ya shirya tsaf kafin ya sake dawowa Najeriya don fuskantar aikin da aka ba shi.  A kan hanyasa ta komawa Turai ne kocin ce ya raste Ingila inda ya fara tuntubar Jordan Ibe don ya shawo kansa ya yi wa Najeriya kwallo.
Jordan Ibe dai dan kwallo ne da ke buga wasa a gaba (striker).

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja