Oliseh ya ki gayyatar Mikel

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh ya ki gayyatar dan kwallon kulob dinChelsea John Mikel Obi a cikin ’yan kwallon da  za su fafata da Tanzaniya a watan gobe a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afirka.A ranar Litinin da ta wuce ne dai Oliseh ya gayyato ’yan kwallo 18 […]

Oliseh ya ki gayyatar Mikel
Oliseh ya ki gayyatar Mikel

Sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh ya ki gayyatar dan kwallon kulob dinChelsea John Mikel Obi a cikin ’yan kwallon da  za su fafata da Tanzaniya a watan gobe a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afirka.
A ranar Litinin da ta wuce ne dai Oliseh ya gayyato ’yan kwallo 18 daga waje inda ya hada su da wadanda ya gayyato a cikin gida.
Wannan shi ne karo na biyu da aka ki gayyatar John Mikel Obi a kungiyar ta Super Eagles.  Idan za a tuna tsohon kocin kungiyar Stephen Keshi bai bayyaci dan kwallon ba a wasan da kungiyar ta yi da Chadi a garin Kaduna a watan Yunin da ya wuce.
Daga cikin ’yan kwallon da Oliseh ya gayyato sun hada da gololi biyu watau  kyaftin bincent Enyeama da Carl Ikeme.  Sai ’yan wasan da suka hada da Izunna Ernest Uzochukwu da Emem Edouk da Sylbester Igboun da Moses Simon.
Sannan an gayyato Godfrey Ogboabonna da Leon Balogun da kuma Keneth Omerou.  Haka kuma akwai Rabi’u Ibrahim da Lukman Haruna da Joel Obi.  Sai Ahmed Musa da Emmanuel Emenike da kuma Anthony Ujah da sauransu.
Tuni ’yan kwallon da ya gayyata suka halarci sansanin horar da su da ke Abuja kafin su tashi zuwa Tanzaniya don fuskantar wasan.