Oloyede, barden yaki da cin hanci

Daya daga cikin al’amuran da suka zama bambarakwai a tarihin aikin gwmanati a Najeriya da ke tashe a ’yan kwanakin nan, shi ne lokacin da Jami’in Hukumar Jarabawar shiga Jami’a ta JAMB a ofishin hukumar da ke Makurdi, Jihar Binuwai, Philomena ta yi ikrarin cewa maciji ya lakume Naira miliyan 36, inda ta bayyana wa […]

Oloyede, barden yaki da cin hanci

Daya daga cikin al’amuran da suka zama bambarakwai a tarihin aikin gwmanati a Najeriya da ke tashe a ’yan kwanakin nan, shi ne lokacin da Jami’in Hukumar Jarabawar shiga Jami’a ta JAMB a ofishin hukumar da ke Makurdi, Jihar Binuwai, Philomena ta yi ikrarin cewa maciji ya lakume Naira miliyan 36, inda ta bayyana wa masu binciken kudi wannan tatsuniyar lokacin da ake gudanar da aikin binciken kudin hukumar bisa umarnin Shugaban Hukumar Jarabawar JAMB, Farfesa Ishak Oloyede.

Kodayake daga bisani Philomena Chieshe ta yi ikrarin cewa ba ta ce maciji ya hadiye kudin ba, hoton bidiyon aikin binciken kudin karkashin jagorancin Oloyede ya tabbtar da cewa tabbas ta fadi cewa ta fadi hakan a wani mawuyacin hali. Ta zargi abokan aikinta da yin “kulunboton” sace kudin da ta adana a asusun ajiya, ta hanyar turo maciji ya lakume su. Mai Magana da yawun Hukumar JAMB Fabian Benjamin shi ma ya tabbatar cewa an samu tafka zamba cikin aminci da mummunar ta’asa a ofishin hukumar na Makurdi.

Mako guda daga bisani, tawagar shugaban hukumar na masu gudanar da binciken kudin sun gano almundahanar Naira miliyan 36, wannan karon a ofishin hukumar JAMB na Jihar Nasarawa. Tsohon jami’in da ke tafiyar da ofishin hukumar a can an zarge shi da sace kudin da aka tara daga sayar da katin rajistar jarabawar hukumar. Jami’in ya yi ikrarin cewa katunan da ba a sayar ba sun kone kurmus a motarsa da ta kama da gobara a wani hadari da ya yi. Sai dai ya kasa bayyana hakikanin gaskiyar lamarin wadanda ya sayar kafin a yi watsi da katunan a karkashin Shugabancin Farfesa Oloyede a Hukumar JAMB. An gano cerwa ikrarin nasa karya ce zunzurunta, bisa la’akari da bayanan da Hukumar JAMB ta tattara a wajen tara bayananta, inda aka gano cewa jerin lambobin katunan da jami’in ya  ce sun kone ta tabbata cewa masu yin jarabawa sun yi amfani da su.

Sai kwatsam wasu labaran biyu da suka zamo bambarakwai suka bayyana. Jami’in Hukumar JAMB na Jihar Yobe, Sanusi Atose, wanda ya kasa bayyana inda kudin hukumar Naira 613,000 suka shige, sai ya zargi kunar bakin waken Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas kan batan dabon kudin. Atose wanda wanda ya bayyana a gaban kwamitin binciken karkashin jagorancin Oloyede, ya yi ikrarin cewa farmakin Boko haram a Jihar yobe ya lalata takardun shigar da kudi banki da rasitai da bayanan hada-hadar ciniki, al’amarin da y ace ya haifar masa asarar takardun tattara bayanan hada-hadar cinikin. Sai dai Oloyede tuni ya yi watsi da ikirarin nasa, inda ya bayar da umarnin ya biya kudin cikin mako guda. Sai kuma Daniel Agbor Jami’in gudanar da ayyukan Hukumar JAMB a Jihar Kogi, wanda ya ce ya kashe Naira biliyan 7 daga kudin JAMB don taimaka wa sauran ma’aikatan hukumar da ke aiki a ofishinsa, wadanda ya ce talauci ya yi musu katutu. Ya ce, “Yanayin ofishin ya kasance dabaibaye da mawuyacin halin talauci, alhali akwai kudi a wajen mu.” Sai ya kara da cewa wasu daga cikin katunan mutanen da ba a san ko su wane ne ba,sun sace su.

Kafin Oloyede ya kama jan ragamar hukumar a amtsayin shugaba a shekarar 2016, masu rubuta jarabawa kan yi amfani da katunan shiga shafukan sadarwar JAMB, ko don yin rajista ko kuma sauran hada-hadar harkokin da suka danganci neman shiga manyan makarantun Najeriya. A cewar Mai magana da yawun Hukumar JAMB, Hukumar Yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC da ’yan sanda an gayyato su don su taimaka wa hukumar gudanarwar wajen gano inda kudin da ake zargin jami’an hukumar sun sace suka makale, a daukacin Hedkwatar hukumar da ke Abuja da ofisoshinta da ke jihohi. Ya ce dimbin almundahanar da aka tafka an yi ne kafin Oloyede ya zama shugaban hukumar.

Ministar kudi Kemi Adeosun ta bayyana wa Majalisr Zartarwa a bara cewa lokacin da Hukumar JAMB karkashin jagorancin Farfesa Oloyede ta zuba wa asusun gwamnatin tarayya Naira biliyan biyar da miliyan 200 cikin shekarar 2017 kadai, inda wannan hukumar dai wadda ta tara Naira biliyan 30 cikin shekara biyar ta zuba Naira biliyan 15 kadai. Adeosun ta ce kudi mafi yawa da JAMB ke zubawa shi ne Naira miliyan uku tun bayan da aka kafa hukumar shekara 40 da suka gabata; wannan wawakeken gibi ya harzuka Hukumar Zartarwa ta binciki kundin bayanan kudin JAMB.

Tabbas Farfesa Ishak Oloyede wani abin misali ne na daban a tsarin aikin gwmanati a Najeriya, wanda ya jajirce wajen zama barde a yakin da ake da cin hanci da rashawa. Ta hanyar jajircewarsa baya ga cewa ya bankado dimbin almundahanar cin hanci da rashawa a JAMB, har ma kara kaimi ya yi wajen shawo kan zamba cikin aminci da sata. Shi gwarzo ne a fafutikar yaki da cin hanci da rashawa, don haka muke shawartar daukacin shugabanni sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati a kasar nan su yi koyi da Farfesa Ishak Oloyede.