Olympiakos ta dauki tsohon dan wasan Madrid Marcelo

Ba zan yi ritaya daga murza leda ba saboda har yanzu akwai gudunmawar da zan bayar a fagen tamaula.

Olympiakos ta dauki tsohon dan wasan Madrid Marcelo

Marcelo

Kungiyar Olympiakos mai taka lada a Girka ta dauki Marcelo, dan wasan Real Madrid da kwantaraginsa ya kare a kungiyar a karshen kakar wasannin da ta gabata.

Rahotonni sun ce ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya a Olympiakos da zabin za a iya tsawaita zamansa idan ya taka rawar gani.

Kungiyar tana ta uku a kan teburin gasar Girka ta Greek Super League bayan wasa biyu da fara kakar nan.

Gabanin daukarsa da Olympiakos ta yi, an ta alakanta dan wasan da kungiyar Leicester City mai buga gasar Firimiyar Ingila.

Mai shekara 34 ya bar Real Madrid a daidai gabar da bukatarsa ta ja baya a kungiyar, inda aka fito da shi sau bakwai kacal a matsayin ’yan wasa zabin farko cikin dukkanin wasanninta a kakar da ta wuce.

Marcelo wanda shi ne dan wasan Real Madrid da ke kan gaba a yawan lashe kofuna a tarihin kungiyar, bayan kaka 15 da ya yi, ya buga a karawa 18 ne kacal a kakar da ta gabata.

Daga cikin manyan kofunan da Marcelo ya lashe a Madrid har da La Liga shida da Kofin Zakarun Turai na Champions League biyar.

Marcelo, wanda ya yi wa Real Madrid wasa 546, ya buga wa tawagar Brazil karawa 58, wadda ya fara taka mata leda a 2006.

A cikin jawabinsa na bankwana yayin barin Los Blancos, Marcelo ya ce bai zai yi ritaya daga murza leda ba saboda har yanzu yana jin cewa akwai gudunmawar da zai bayar a fagen tamaula.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna