Olympics: Rashin shugabanni nagari ya shafe mu — Obi
Ɗan takarar ya ce akwai buƙatar a ɗauki wasu darusa dangane da gaza yin kataɓus da Najeriya ta yi.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce akwai buƙatar Najeriya ta ɗauki darasi dangane da rashin taɓuka abun arziƙi a gasar Olympics da aka kammala a birnin Paris ta 2024.
A cikin jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, tsohon gwamnan Anambra, ya ce har yanzu ƙasar ta samu wasu nasarori masu inganci duk da rashin nasarar da ta samu.
- Ambaliya: Mutum 3 sun rasu, dubbai sun rasa muhalli a Bauchi
- Ambaliyar ruwa ta raba mutum 100 da muhallansu a Jigawa
Sai dai ya buƙaci ‘yan Najeriya da su kawar da kawunansu daga shugabannin siyasa marasa nagarta, domin suna da illa fiye da alhairin da suke so ga ƙasa.
“Zan so ’yan Najeriya ka da su yi watsi da saƙon nan mai ƙarfi daga gasar wasanni na duniya.
“Yayin da babbar ƙasa a nahiyar Afirka ta ƙare ba tare da samun ko kyautar lambar yabo ɗaya ba, inda ƙasashen Afirka tara suka samu lambobin yabo, duk da haka Najeriya tana da abubuwa masu kyau a gasar ta duniya duk da ƙalubalen da muke fuskanta.
“’Yan Najeriya sun fito suna haskawa a gasar Olympics saboda sun samu horo a wurare masu kyau, inda ake gane hazaƙarsu kuma ƙasashe suna ɗaukar su da muhimmanci.”