OPEC ta rage danyen mai da Najeriya za ta rika hakowa
Kungiyar OPEC ta rage ganga 300,000 daga yawan danyen mai da Najeriya za ta riko hakowa a kullum daga shekarar 2024
Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai (OPEC) ta zaftare ganga dubu 300 daga yawan danyen mai da Najeriya za ta rika hakowa a kowacce rana daga shekarar 2024.
Yanzu danyen mai da Najeriya za ta rika hakowa kullum a 2024 zai ragu zuwa ganga miliyan 1.5 da daga miliyan 1.8 da ta saba hakowa a 2023.
Matakin na OPEC na ya shafi kasashe da dama, ciki har da Angola da Congo da su ma suke samar da danyen mai daga nahiyar Afirka.
A sabon tsarin rage danyen mai da kasashe ke fitarwa, Angola za ta koma hako ganga miliyan 1.1, Congo kuma ganga 225,000 a kullum.
- Za a fara yi wa masu fyaɗe dandaƙa a Kaduna
- Yadda ’Yan Damfara Suka Tura Mana Rasit Da ‘Alat’ Din Bogi
Wannan mataki ya biyo bayan taron OPEC kan daidaita farashin danyen mai a kasuwannin duniya da ya gudana birnin Geneva.
Kungiyar ta bukaci kamfanoni 3 masu zaman kansu (IHS da Rystad Energy da Wood Mackenzie) su sanya ido wajen tabbatar da bin umarnin a Najeriya, Angola da Congo.
Kafin taron dai , Najeriya ba ta iya hako danyen mai ganga miliyan 1.580 da OPEC ta kayyade mata, saboda matsalar tsaro.
Haka ita ma Angola ta gaza cimma nata adadin danyen man na ganga miliyan 1.280.
Najeriya dai na ta kokarin kara yawan man da take hakowa da nufin kara kudaden shigarta, inda take kokarin tabbatar da tsaro a yankin Neja Delta da kuma dakile masu fasa bututun mai suna sata.