Open Diaries: Sanya N3,000 kudin rijista a dandalin Whatsapp ya bar baya da kura

Shafin zamantakewar aure na Open Diaries ya sanya N3,000 a matsayin kudin rijista

Open Diaries: Sanya N3,000 kudin rijista a dandalin Whatsapp ya bar baya da kura

Hoto: Shafin Open Diaries.

Shafin koyon zamantakewar aure na Open Diaries a kafafen sada zumunta ya sanya N3,000 a matsayin kudin rijista domin shiga dandalinsa na Whatsapp.

Fatima Fouad Hashim wadda ake wa lakabi da Oum Malak ita ce mai shafukan Open Diaries, a kafofin sada zumunta na Whatsapp da Instagram da kuma Facebook.

Open Diaries dandali ne da mutane ke bayyana sirrin rayuwarsu tare da neman shawara ko karin bayani a kan wani sha’ani da ya shafi rayuwarsu, musamman na zamantakewar aure.

Sai dai da dama daga cikin mambobin dandalin sun nuna rashin amincewarsu a kan sanya kudin rajistar, inda suke ganin babu wani dalili da zai sa a caje su kudi.

Amma Oum Malak, wadda ta ce tuni aka cika dandalin Open Diaries biyar na WhatsApp, ta nanata cewa babu abin da zai sa ta sauya ra’ayi a kan biyan kudin rajista.

Daya daga cikin mambobin, Mariya Salis Ibrahim, ta ce ba za ta iya biyan kudin rajista N3,000 don shiga dandalin WhatsApp ba, alhali akwai wasu dandalin na kyauta wadanda kuma sun fi amfani.

Ta kara da cewa, babu abin da mai dandalin ke tabukawa a cikin group din domin su ne ke sanya bayanai da kansu, su kuma tattauna a tsakaninsu. To me yasa zaa  rika biyan N3,000 a duk shekara?

Ita ma wata mai bibiyar shafin, Hafsat Muhammad, ta ce da wannan kudin shiga Fatima ba ta bukatar sake yin wata sana’a, domin zata rika samun kusan Naira miliyan hudu a duk shekara daga kafofi biyar na WhatsApp da take da su wadanda gaba daya a cike suke.

Sai dai kuma, wani mai shafin Istagram na “Fantasiescollections”, ya ce abin mamaki ne ganin yadda mutane ke ta korafi saboda Naira 250 a kowane wata, yana mai cewa: “Bayan na karanta maganganun jama’a, sai na  lissafa naga  cewa N250 ne kawai a kowane wata.