Ortom ya yi watsi da shirin gwamnati na kafa wuraren kiwo

Gwamnan Jihar Benuwe, Sam Ortom ya gana da shugaba Muhammadu Buhari kuma ya yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na kafa wuraren kiwon shanu a jihar.   Gwamnan ya ziyarci Buhari a fadarsa da ke Abuja kan kashe-kashen da ake zargin fulani makiyaya ke yi a wasu sassan jihar.   Ministan Albarkatun Noma, Audu Ogbe […]

Ortom ya yi watsi da shirin gwamnati na kafa wuraren kiwo

Gwamnan Jihar Benuwe, Sam Ortom ya gana da shugaba Muhammadu Buhari kuma ya yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na kafa wuraren kiwon shanu a jihar.
 
Gwamnan ya ziyarci Buhari a fadarsa da ke Abuja kan kashe-kashen da ake zargin fulani makiyaya ke yi a wasu sassan jihar.
 
Ministan Albarkatun Noma, Audu Ogbe ya fada a ranar Litinin din da ta gaba cewa Gwamnati za ta kafa wuraren kiwon shanu don maganin rikicin fulanin da manoma a kasar baki daya.