Orubebe ya zama jagoran yakin neman zaben APC a Delta

Orubebe zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna na APC a Jihar Delta, Sanata Ovie Omo-Agege

Orubebe ya zama jagoran yakin neman zaben APC a Delta

Godsday Orubebe

An nada tsohon Ministan Harkokin Neja-Delta, Godsday Orubebe, a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Delta a zaben 2023, Sanata Ovie Omo-Agege.

Kakakin Omo-Agege, Ima Niboro, ya ce dan takarar ya nada tsohon ministan ya jagoranci kwamitin yakin neman zabensa ne bisa la’akari da irin gogewarsa da kimarsa da kuma basirarsa, domin kaiwa ga nasara.

“Za mu yi aiki tare da Orubebe wajen jagorantar muhimman tsare-tsare da kuma tuntuba, duba da yadda ya lakanci takun Jam’iyar PDP.

“Za mu kuma yi aiki da sauran mambobin kwamitin yakin neman zaben wajen ganin PDP ta kwashi kashinta a hannu, ta fice daga fadar gwamnatin Jihar Delta ranar 29 ga watan Mayu, 2023,” inji sanarwar da Niboro ya fitar.

Ya ci gaba da cewa, “Tafiya tare da shi ta kara wa kwamitin karfi da kuma kara kafa tafiyar domin kaiwa ga nasara a zaben dake tafe.’’

Idan ba a manta ba, a watan jiya ne Mista Orubebe ya fice daga PDP bayan an fitar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar.

Sunan tsohon ministan ya yi tambari a kafofin yada labarai ne yayin Zaben Shugaban Kasa na 2015 lokacin da ya yi yunkurin ta da yamutsi a dakin tattara sakamakon zabe, yana zargin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da taimaka wa APC.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi