Oshimhole ya shawarci Kiristoci masu zuwa ibada a Isra’ila
Gwamnan Jihar Edo Comrade Adams Oshiomhole ya shawarci Kiristoci masu zuwa aikin hajji a kasar Isra’ila da Rum da su kasance masu nuna kyakkyawar halayya, tare da kare mutuncin kansu da kasa Najeriya baki daya.Gwamnan ya yi wannan kira ne a Cocin (Mathews Anglican church da ke Bernin, fadar gwamnatin jihar ya umarci masu zuwa […]
Gwamnan Jihar Edo Comrade Adams Oshiomhole ya shawarci Kiristoci masu zuwa aikin hajji a kasar Isra’ila da Rum da su kasance masu nuna kyakkyawar halayya, tare da kare mutuncin kansu da kasa Najeriya baki daya.
Gwamnan ya yi wannan kira ne a Cocin (Mathews Anglican church da ke Bernin, fadar gwamnatin jihar ya umarci masu zuwa aikin ibadar su dauki wannan tafiyar a matsayin ibada, inda ya ce: ‘’ku kasance masu kankantar da kawunanku ga Ubangiji a wannan kasa tsarkakakkiya, sannan kuma ya kara da cewa, lallai ba wai kuna wajen domin koyo ba, amma domin sanin Allah da kuma dawowa a matsayin shiryayyu’’.
Daga nan sai ya taya wadanda suka samu damar zuwa wannan aiki na ibada na wannan shekara ta 2014 murna da irin kokarinsu da ya ce suka yi, amma wasu ba su samu damar zuwa ba saboda wasu dalilai na rashin kudi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sakataren mahajjata na Kiristoci na Jihar Sir, Patrick Ihayere ya ce: ‘’ Mai girma gwamna na gabatar maka da su, wato Maza da Mata wadanda za su je aikin hajji domin rokon Allah da neman shiriya ya kara da ce wa muna da mutane tsakanin maza da mata su 83, wadanda a halin yanzu mun rigaya mun tantancesu, kuma za mu yi iya kokarinmu domin tabbatar da sun samu zuwa gaba dayansu ba tare da an bar kowa a baya ba,” inji shi.
…..Ya kaddamar da cibiyar karbar maganin ciwon suga kyauta a Benin
Daga Abubakar AbdurRahaman Masagala a Benin
Gwamnan Jihar Edo kwamared Adam Oshiomhole ya kaddamar da cibiyar karbar maganin ciwon suga kyauta, domin taimaka wa masu fama da cutar . Gwamnan ya kaddamar da wannan cibiyar ne a Babban asibitin Benin a tsakiyar makon da ya gabata, kuma an kasa shi a wurare guda uku, wato na daya a Central Hospital na garin Benin, sai na biyu a Central Hospital na garin Uromi na ukun a central Hospital na garin Auchi; kuma wannan tallafin an yi shi ne tare da hadin kan Kamfanin Harhada magunguna na Nobo,Nordisk,Pharma,Gulf.
Da take tofa albarkacin bakinta Kwamishinar lafiya ta jihar, Mrs Aihanuwa Eregie ta ce cutar suga cuta ce wadda ta shafi al’umma da dama, kuma a lokuta da dama. Don haka a cewarta ba za a iya a ce an warkar da cutar gaba dayanta ba ajikin wanda yake fama da ita, amma ana iya a rage kaifinta, ta yadda mai fama da ita zai samu sauki, inda ta kara da cewa, lallai wannan ciwon yana daga cikin cututtuka guda shida mafi hadari ga rayuwar bil Adama, mai rage tsawon rayuwar mutane da hallakarwa.
A bayaninsa Sakataren bangaren asibitoci na jihar Dokta Ofure Ebobeime ya gode wa wadannan kamfuna bisa hadin kai da suka bai wa gwamnatin jihar, domin samar da ingantattun magunguna domin ganin an samu an rage kaifin wannan cutar ga masu fama da ita.
Yayin da shugaba bangaren masu kula da asibitocin jihar Dokta Ebeghe Amadasun, wanda Yarima Lai Momoh ya wakilta a wajen kaddamarwar, ya ce ina kirga wadanda aka danka wa wannan aiki a hannunsu da su tabbatar sun tafiyar da aikin cikin gaskiya, su rika bai wa mutane masu fama da wannan cutar maganin tare da kyakkyawar kulawa.