Oshiomhole: Gwamnonin APC 16 sun gana da Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC 16, rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da ganawar ne don sanin matsayin shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole da aka dakatar. Gwamnonin da suka halarci ganawar da shugaba Buhari sun hada da: Borno, Legas, Ogun, Edo, Kebbi, Jigawa, Kwara, Nasarawa, Neja, Filato, Ondo, Kano, Osun, Katsina, da Imo, […]

Oshiomhole: Gwamnonin APC 16 sun gana da Buhari

Gwamnonin APC 16 da suka gana da Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC 16, rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da ganawar ne don sanin matsayin shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole da aka dakatar.

Gwamnonin da suka halarci ganawar da shugaba Buhari sun hada da: Borno, Legas, Ogun, Edo, Kebbi, Jigawa, Kwara, Nasarawa, Neja, Filato, Ondo, Kano, Osun, Katsina, da Imo, da jihar Gombe.

A cikin Gwamnonin APC 20, hudu ne kadai ba su halarci ganawar ba, wadanda suka hada da: Kaduna, Yobe, Kogi, da Ekiti.