Oshiomhole ya caccaki gwamnoni Daga Bashir Liman, Jos Gwamna Adams Oshiomhole na Jihar Edo ya caccaki matsayin da gwamnonin qasar nan suka xauka na cewa ba za su iya biyan Naira dubu 18 a matsayin mafi qarancin albashin ma’aikata ba, inda ya ce ya zama
A makon da ya gabata ne Majalisar gwamnonin qasar ta bayyana cewa saboda halin da tattalin arzikin qasar nan ke ciki zai yi wa gwamnoni wahala su ci gaba da biyan mafi qarancin albashi na N18,000, wannan matsayi na gwamnonin ya sha suka a wurin mutane da dama, musamman ma’aikata. Sai dai kuma gwamnonin jihohin […]

A makon da ya gabata ne Majalisar gwamnonin qasar ta bayyana cewa saboda halin da tattalin arzikin qasar nan ke ciki zai yi wa gwamnoni wahala su ci gaba da biyan mafi qarancin albashi na N18,000, wannan matsayi na gwamnonin ya sha suka a wurin mutane da dama, musamman ma’aikata. Sai dai kuma gwamnonin jihohin Edo da Filato da Ogun sun ce ba su tare da wannan matsayi na ’yan uwansu.
Oshiomhole ya caccaki gwamnoni
Gwamna Adams Oshiomhole na Jihar Edo ya caccaki matsayin da gwamnonin qasar nan suka dauka na cewa ba za su iya biyan Naira dubu 18 a matsayin mafi qarancin albashin ma’aikata ba, inda ya ce ya zama dole su biya wannan albashin domin rashin biyan ba zai farfado da tattalin arzikin qasar nan daga mawuyacin halin da ya samu kansa a ciki ba.
Gwamnan ya tunatar da gwamnonin cewa an cimma yarjejeniyar biyan mafi qarancin albashin ne tsakanin qungiyoyin qwadago da kuma gwamnatocin da suka gabata, hakan ya sanya Gwamna Oshiomhole ya jaddada wa gwamnonin da sauran masu riqe da muqaman siyasa cewa, ba za a tafiyar da demokuradiyya bisa son ransu da jin dadinsu ba.
Gwamnan na Edo ya bayyana matsayinsa ne a yayin wani taron na masu ruwa da tsaki na Qungiyar Qwadago ta Najeriya (NLC) da aka yi don sasanta shugabannin bangarorin qungiyar biyu, wato tsakanin Kwamared Ayuba Wabba da Joe Ajaero, tun bayan da rikici ya barke sakamakon zaben da qungiyar ta gudanar watanni shida da suka gabata.
A lokacin da yake jawabi yayin taron da aka gudanar a Labour House da ke Abuja, Gwamna Oshiomhole ya ce babu wanda zai ga baiken biyan ma’aikata Naira dubu 18 a matsayin mafin qarancin albashi a qasar nan, saboda ba tilasta wa gwamnati aka yi ba, a’a, yarjejeniya ce tsakanin gwamnati da kuma qungiyar qwadago.
Ya ce: “Ni cikakken dan qwadago ne, na fito qarara na fada wa gwamnoni ’yan uwana cewa, a matsayinmu na wadanda suke neman mafita dangane da matsalar da muke fuskanta, ya zama dole mu nazarci al’amarin, ba kawai mu riqa ganin baiken batun biyan mafi qarancin albashi da aka amince da shi a qasa ba. Na shiga dandazon mambobin qungiyar qwadago inda muka gudanar da zanga-zanga a lokacin da majalisar tarayya take yunqurin canza kundin tsarin mulki don a mayar da biyan mafi qarancin albashi a matsayin yawan samun kudin gwamnati, yanayin biyan albashi.
“Na ce musu ma’aikata zaqaqurai ne a demokuradiyya, su ne za su bazama kan tituna don gudanar da zanga-zanga, za su kuma yi zanga-zangar ne don demokuradiyya. Ba za a kuma tafiyar da demokuradiyya daidai da son rai ko jin dadin gwamnoni ko ministoci ko shugabannin qasashe ba,” inji shi.
Ya ce: “Ina da yaqinin matsalar da shafi tattalin arziki ba ta shafi biyan mafi qarancin albashi ba. Nakan yawaita tunatar da ’yan uwana cewa ba a tilasta biyan mafi qarancin albashin ba, an cimma yarjejeniya ne sannan gwamnatocin jihohi suka amince da hakan, shugaban qasa ya sanya hannu ba wai don an tilasta masa ba, ba a yi yajin aikin da ya tilasta wa shugaban qasa na lokacin sanya hannu a kan yarjejeniyar ba, ya sa hannu ne don radin kansa.
“Na tabbata idan aka kalli Naira dubu 18 a matsayin mafi qarancin albashi, sannan aka kwantanta kudin da ake canja Dala a yanzu, na tabbata kudin bai kai Dala 100 ba. Ina tsammanin za a iya cewa dala 80 ne, to ka raba Dala 80 da kwana 31 a wata, za ka samu Dala biyu da wani abu ne. Babu wanda zai ce bai kamata ma’aikata su riqa karbar Dala da 2 da wani abu kowace rana a matsayin kudin albashinsu ba, don haka ba zan yarda da batun rage albashin ma’aikata ba, saboda gwamnati mai adalci ita take sanya jin dadin mutanenta a zuciya,” inji shi.
Duk da cewa Oshiomhole ya yarda cewa tattalin arzikin qasar nan yana cikin mawuyacin hali, amma ya tabbatar da matsalar ba ta yi qamarin da za ta sa gwamnonin qasar nan har su yunqurin saba yarjejeniyar biyan mafi qarancin albashi da gwamnati da qungiyar qwadago suka sanya wa hannu ba
Ya ce: “Tabbas akwai matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin qasar nan, akwai kuma matsalolin da suka dabaibaye yadda ake tafiyar da tattalin arzikin, tabbas an yi sama da fadi da wandaqa da dukiyar qasa, qorafina kawai shi ne qungiyar qwadago ba ta iya daga murya sosai kan batun satar dukiyar qasa da aka yi a lokacin da ake yi ba. Zan iya cewa qungiyar qwadago ta yi babban laifi a wannan bangaren. A lokacin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya fasa qwan batan wadansu kudi, ya kamata qungiyar qwadago ta y i babatu a kan batun, sai suka yi shiru, na kuma riqa nanata cewa duk wani abu da manya za su yi, kaidin na qarewa a kan talakawa ne.
“Ya zama dole NLC ta riqa tuhumar duk wani shiri da aka kawo da aka san zai quntata wa talakawa a nan kusa ne ko a gaba. Wahalar da ake sha yanzu a sakamakon satar dukiyar qasar nan da wandaqa da ita da aka riqa yi ne da kuma rashin iya tafiyar da tattalin arzikin qasar nan. Kada a manta gangar mai ta kai Dala 108, amma a yanzu tana qasa da Dala 50, an samu faduwar samar da Dala 50, dole a sha wahala,” inji shi.
A yanzu ana neman maqudan kudi don a biya basussukan da ake bi, “sannan a samu kudin da za a gudanar da wadansu ayyukan, duk da cewa farashin mai yana dada faduwa, ko da an daina biyan albashi kwata-kwata ne, hakan ba zai sa a fita daga cikin matsalar da ta dabaibaye tattalin arzikin qasar nan ba.”
Qarin albashi ma’aikaci ke buqata – NLC
A lokacin taron masu ruwa da tsakanin Qungiyar Qwadago ta Najeriya (NLC) shugaban bangare na qungiyar, Kwamared Wabba ya qi amincewa da yunqurin gwamnoni na rage albashin ma’aikata
Ya ce: “Ba za mu taba amincewa da wannan batun ba, ma’aikata a Najeriya ba za su taba yarda da wannan batun ba. Ba mu ne matsalar ba, mu ne ma wadanda za su shawo kan matsalar. Matsalar ita ce har yanzu ba su rage kudin da suke kashe wa kansu wajen tafiyar da mulki ba, ya kamata su je su rage kudadensu na bangaren tsaro. Sannan su rage kudin da suke kashe wa tawagarsu ta hanyar tafiye-tafiye, sannan ya zama dole su yi wa wadanda suka zabe su cikakken bayanin kudin da gwamnati take kashewa. Za mu tsaya kai da fata don yin jayayya da duk wani yunquri na rage albashin ma’aikata ta kowace hanya.
“Kada su manta an cimma yarjejeniyar biyan mafin qarancin albashi na Naira dubu 18 ne bisa doron za a iya sake duba batun ganin an yi qari a kan hakan ba wai ragewa ba. A yanzu za mu gudanar da shirye-shirye don ganin an qara wa ma’aikata albashi tun da batun yarjejeniyar ya amince da hakan,” inji shi.
Ango ga Gwamnoni: Duk wanda ba zai iya mulki ba ya yi murabus
Shugaban Qungiyar Dattawa Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya ce duk wani gwamnan da ba zai iya biyan Naira dubu 18 a matsayin mafi qarancin albashin ma’aikata ba, to ya yi murabus don ya ba masu son kyautata wa ma’aikatan Najeriya.
Farfesa ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da jaridar banguard, inda ya bayyana cewa gwamnoni sun ba shi kunya, ba su tausayin ma’aikata, sannan ya buqaci kada ’yan Najeriya su amince da batun duk wani gwamna da ba ya kishin al’ummarsa duk da irin muqadan kudade da suke shiga aljihun gwamnonin duk wata.
Farfesa Ango wanda tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ne ya bayyana rashin jin dadinsa sakamakon yadda kowane wata gwamnoni suke karbar biliyoyin Naira don batun tafiyar da sha’anin jiharsu, sannan ba a tuhumar yadda suke kashe wannan kudi, amma don rashin tausayi za su ce ba za su iya biyan Naira dubu 18 a matsayin mafi qarancin albashi ga ma’aikata a wata ba.
Ya ce duk wani gwamna da bai yi murabus ba, sannan ya ci gaba da cewa ba zai iya biyan mafi qarancin albashin ba, to ma’aikatan Najeriya su yi watsi da shi.
“Idan har wadanda gwamnoni suka nada muqaman siyasa za su iya samun Naira miliyan 1 kowane wata, to ta yaya wadannan gwamnoni za su ce ba za su iya biyan Naira dubu 18 a matsayin mafi qarancin albashi ga kowane ma’aikaci da yake yi wa jiha aiki ba?
Farfesa Ango ya buqaci gwamnonin Najeriya 36 da su rage kashe kudin da suke samu da kashi 50 cikin 100 don a samu kudin da za a riqa gudanar da ayyuka a jiharsu.
Karnukan gwamnoni na laqume fiye da dubu 18 a wata – Murray-Bruce
dan Majalisar Dattijai mai wakiltar mazabar Bayelsa ta Gabas, Ben-Murray Bruce, ya ce ana kashe fiye da Naira dubu 18 wajen kula da karnukan da ke gidajen gwamnati a daukacin fadin qasar nan, don haka zalunci ne ga gwamnonin da ke qoqarin ganin an rage mafi qarancin albashi na Naira dubu 18.
dan majalisarwanda ya yi bayanai da dama a shafinsa na twitter, ya ce shirme a ce ana biyan ma’aikacin yi wa qasa hidima na NYSC kimanin abin da ya kai Naira dubu 20 a wata, amma ma’aikacin gwamnati da ke da iyali an hana su mafi qarancin albashi na Naira dubu 18.
Ya ce bisa la’akari da matsananciyar tsadar rayuwa a qasar nan, babu wani alfanu idan aka rage albashi mafi qaranci na Naira dubu 18.
Ya yi nuni da cewa, “Ina da masaniyar cewa hatta karnukan da ke gidajen gwamnatocin ana kashe musu fiye da Naira dubu 18 wajen kula da su a kowane wata. Shin ba mutum ya kamata a bai wa cikakkiyar kulawa ba?
“Wannan rashin adalci ne ga gwamnati har ta yi tunani rage albashin ma’aikata daga Naira dubu 18. Shin me ma wadannan kudi za su iya saye a Najeriya ta yau?
“Ma’aikacin da ke da iyali, yana daukar kudin da ba su kai abin da ake biyan mai yi wa wasa hidima ba, wanda ke daukar kimanin Naira dubu 19,800. Rage masa kudi dai rashin tunani ne. Mutumin da ke daukar Naira dubu 18 yana fama da yadda zai biya kudin haya, ya ciyar da iyali, sannan ya biya kudin makaranta. Rage masa albashi tamkar azabtar da iyalansa ne.