Oshiomhole ya gano malamar makaranta da ba ta iya karatu ba

Yunkurin tantance takardun shaidar malaman makarantun firamare a Jihar Edo da Gwamnan Jihar Kwamared Adams Oshiomhole ya ba da umarni ya fara haifar da da mai ido, inda Gwamnan da kansa ya gano wata malamar makaranta da ta kasa karanta wata takarda daga cikin takardunta.Wannan abin kunya ya faru ne a makarantar firamare ta Asologun […]

Oshiomhole ya gano malamar makaranta da ba ta iya karatu ba

Gwamna Adams Oshiomhole na Jihar EdoYunkurin tantance takardun shaidar malaman makarantun firamare a Jihar Edo da Gwamnan Jihar Kwamared Adams Oshiomhole ya ba da umarni ya fara haifar da da mai ido, inda Gwamnan da kansa ya gano wata malamar makaranta da ta kasa karanta wata takarda daga cikin takardunta.
Wannan abin kunya ya faru ne a makarantar firamare ta Asologun da ke karamar Hukumar Ikpoba Okha da ke birnin Benin, lokacin da malamar mai suna Misis Augutsa Odemwingie ta kasa karanta wata takardar rantsuwa da ta gabatar a matsayiin daya daga cikin takardunta.
Gwamna Oshiomhole wanda ya kai ziyarar ba-zata ce zuwa Cibiyar Horar da Ma’aikata ta Jihar, inda ake tantance malaman, ya kadu ganin malamar ta kasa karanta takardar inda ya ce: “Idan ba ki iya karatu ba, me kike koyar da yara, me kike rubutawa a kan allo?”
Lokacin da Gwamnan ya isa cibiyar ya dauki lokaci yana duba takardun shaidar da malaman suka gabatar.
Kuma matsala ta taso ne a lokacin da aka zo tantance Misis Odemwingie, inda Gwamnan ya nemi ta karanta takardar rantsuwar da ta gabatar. Malamar sai ta shiga inda-inda yayin karanta takardar a gaban jama’a kamar mai koyon karatu a ajin renon yara.
Shugaban kungiyar kungiyar Malaman Makaranta ta Najeriya (NUT) Reshen Jihar Kwamared Ikosimi wanda ya bayyana gazawar Misis Odemwingie a matsayin abin kunya, ya ce kungiyar tana goyon bayan yunkurin gwamnatin jihar na tsabtace harkokin makarantun jihar.
Ya ce, “Muna hada hannu da gwamnati domin sake farfado da harkokin ilimi a jihar. Abin da malamar ta nuna yanzu abin kunya ne, ya nuna tabarbarewar ilimi. A matsayina na Shugaban NUT na rubuta wa Gwamnan cewa muna ba da cikakken goyon baya ga abin da yake yi. Kuma ya sanya NUT a cikin lamarin domin bankado masu laifi wadanda ba su da wani amfani a bangaren ilimi.”