Osimhen da Asisat Oshiola sun zama gwarazan ’yan wasan Afirka na 2023
Victor Osimhen ya zama dan Najeriya namiji na farko da ya lashe kambin a shekaru 24, yan Kanu Nwanko da ya lashe a 1999
Dan wasan gaban Super Eagles, Victor Osimhen ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasn Afrika na 2023, wanda hakan ya daga darajarsa a jerin manyan ’yan wasa na duniya.
A bangaren mata kuwa, Asisat Oshiola ta Kungiyar Super Falcon ta Najeriya kuma mai taka leda a kungiyar Barcelona ce ta zama gwarzuwar ’yar wasan Afirka a bana.
- Tubar ’Yan Kalare Ta Rage Kwacen Wayoyi Da Haura Gidaje a Gombe
- Daliban jami’ar da aka sace a Nasarawa sun kubuta
Karon farko ke nan tun shekarar 1999 da wani dan wasa daga Najeriya ya lashe kyautar a bangaren maza, bayan Kanu Nwankwo shekaru 24 da suka gabata.
Osimhen wanda ke taka leda a Napoli ya doke Achraf Hakimi na kasar Morocco da Mohamed Salah na Masar wajen lashe kyautar ta gwarzon Afrika.
Bajintar da Osimhen ya yi a kakar wasa ta bara wajen taimakawa Napoli ta lashe gasar Serie A ta kasar Italiya, ya ba shi damar lashe kambun.
Dan wasan ya jefa wa Napoli kwallo 26 a gasar ta Italiya kuma ya zama dan wanda da ya fi jefa kwallo a karshen kakar.
An gudanar da bikin karrama gwarzon dan wasan na Afrika ne a birnin Marakesh na Morocco.