Osimhen: Mai tallan burodi da ya zama dan kwallo mafi daraja a Afirka
Yanzu haka darajarsa ta kara karfi, inda manyan kungiyoyi a Turai suke rububinsa.
A watan Fabrairu ne Kungiyar Kwallon Kafa ta Napoli ta Italiya ta yi bikin kalankuwa.
Abin mamaki, a bikin yara masoya kungiyar sun rika sanya fentin baki a jikinsu tare da sanya takunkumin fuska domin su yi kamanceceniya da dan wasan Najeriya, Victor Oshimhen.
- Dalilin da aka kai samame gidan Matawalle — Gwamnatin Zamfara
- Mutumin da ya yi kisa shekara 15 da suka wuce ya kai kansa ga ’yan sanda
Fitaccen mawakin Italiya, Alex Garini ma ya rera waka game da dan wasan.
Yanayin yadda ya nuna bajinta a kakar bana, ya sa kungiyoyin Turai da dama suka fara zawarcinsa.
A kakar bana, dan wasan na Najeriya ya lashe kyautar takalmin zinare a Italiya, bayan ya zama dan wasan da ya ci mafi yawan kwallaye a gasar Serie A.
Nasarar dai ta ba shi damar kafa tarihin zama dan Afirka na farko da ya kai ga kafa wannan tarihi.
Karin tarihin da Osimhen ya kafa kuma shi ne zama dan wasa na farko da ya samu nasarar hade kyautar takalmin zinare da kuma lashe Kofin Serie A a lokaci guda, da ake kira da ‘Scudetto’ tun shekarar 2009, lokacin da Zlatan Ibrahimobic ya kafa nasa tarihin a Kungiyar Inter Milan.
Kwallaye 25 Osimhen ya ci a kakar bana, yayin da mai biye da shi Lautaro Martinez na Inter Milan ke da kwalllaye 21.
A yanzu Osimhen ne dan wasan Napoli na hudu da ya lashe Kofin Serie A da kuma kyautar yawan kwallaye, inda ya bi sahun Diego Maradona da Edison Cavani da Gonzalo Higuain.
Tuni Shugaban Kungiyar, ya fara yi wa manyan kungiyoyin duniya kashedi.
Aurelio De Laurentiis, ya ce ba zai sayar da Victor Osimhen ba a kasuwar bazarar musayar ’yan wasa ba.
Osimhen ba zura kwallo kawai yake yi ba, matashin dan wasan yana matukar ji da karfi. Yadda yake zagayawa a fili abin a yaba ne.
Yana zuwa gaba ya zura kwallo, sannan ya dawo ya hana ci, sannan bai cika buga fanareti ba, domin wasu ’yan wasan su samu su zura kwallo.
Wannan ya sa magoya bayan kungiyar ke matukar kaunarsa. Hadakarsa da dan wasan gaba na kasar Georgia, Kvicha Kvaratskhelia ya samu tagomashi, inda su biyun suke haduwa su azabtar da masu tsaron bayan kungiyoyin Italiya da Turai a Gasar Zakarun Turai.
Kamar yadda Hausawa ke cewa ba rabo da gwani ba, Kungiyar Napoli dai tun rashin gwaninta, Diego Maradona, ba ta sake samun wani gwanin ba kamar Osimhen.
Osimhen dan asalin Legas ne da ya taso yana sayar da ruwan leda da burodi a titunan Legas, inda yake bin motoci da gudu yana sayar da hajarsa.
A lokacin saboda talauci, iyayensa sai da suka kasa biyan kudin haya, wanda hakan ya sa dole suka koma rara-gefe a gidajen wucin-gadi a kusa da bolar Olusosun, daya daga cikin manyan wuraren zuba shara a Najeriya, inda a kullum suke fargabar gwamnati za ta iya rusa gidajen ta kore su.
Tun yana karami mahaifiyarsa ta rasu ta bar su, su bakwai da mahaifinsu, inda suka taso cikin wahala da talauci.
Osimhen ya fara da buga wa Najeriya wasa ne a kungiyar ’yan kasa da shekara 17, inda ya ci kwallo 10 sannan ya jagoranci Najeriya lashe kofi na biyar.
Bayan gasar ce ya samu kwantaragi da Kungiyar Wolfsburg na shekara uku da rabi.
Daga farawa ya samu rauni, inda ya yi fama da jinya da ta sa ya buga wasa 12 a gasar Bundesliga, amma bai zura kwallo ko daya ba.
Wannan ya sa dan wasa ya shiga damuwa, amma bai cire tsammani ba A shekarar 2018 ce dan wasan ya koma Kungiyar Sporting Charleroi ta Belgium, inda ya zura kwallo 20 a wasa 36.
A shekarar 2019 kuma ya koma Kungiyar Lille ta Faransa a kan Fam miliyan 12, inda can ma ya zura kwallo 18 a wasa 38.
A shekarar 2020 kuma, dan wasan ya koma Kungiyar Napoli, inda kungiyar da zare makudan kudi Fam miliyan 70 wajen dauko shi, inda ya zama dan wasan Afirka mafi daraja har zuwa yanzu.
Yanzu haka darajarsa ta kara karfi, inda manyan kungiyoyi a Turai suke rububinsa.