Osimhen ya maka ɗan jarida a kotu

Osimhen ya garzaya kotu ne don ya wanke kansa daga yunƙurin ɓata masa suna.

Osimhen ya maka ɗan jarida a kotu

Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke buga wasa a ƙungiyar Galatasaray Victor Osimhen, ya shigar da ƙarar wani ɗan jaridar Turkiya Tolga Bozduman bisa zargin ɓata masa suna.

A cikin wani saƙo da wani makusancin Osimhen ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a fara sauraron ƙarar da ɗan wasan ya shigar bayan da ɗan jaridan ya zarge shi da naushin sa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ɗan jarida Bozduman ya zargi Osimhe da cin zaraginsa, bayan tashi wasa 3-3 tsakanin ƙungiyarsa ta Galatasary da kuma Dynamo Kyiv.

Yanzu haka dai Osimhen na fuskantar bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kai.

A makon da ya gabata ne dai dama labarin naushin ɗan jaridan ya fito, inda rahotanni suka nuna cewar Osimhen ya nemi ya bai wa ɗan jaridan kuɗi don ya goge hoton amma ya ƙi amincewa.

Osimhen mai shekaru 26 ya ƙaryata dukkanin zarge-zargen da ake masa, inda ya ce ya garzaya kotu ne don ya wanke kansa daga yunƙurin ɓata masa suna.

 

Osimhen ya maka ɗan jarida a kotu

Abba ya karrama fitattun Kanawa 35

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa

Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu