Osinbajo da ministoci sun gudanar da bikin littafi ta duniya

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Ministan Birnin Tarayya na Abuja, Malam Muhammad Musa Bello sun gudanar da bikin ranar littafai da ’yancin dab’i ta duniya tare da daliban makarantar firamare da ke unguwar Life-Camp a Abuja. kungiyar da ke rajin ganin ana karance-karance da ake kira “Rainbow Book […]

Osinbajo da ministoci sun gudanar da bikin littafi ta duniya

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Ministan Birnin Tarayya na Abuja, Malam Muhammad Musa Bello sun gudanar da bikin ranar littafai da ’yancin dab’i ta duniya tare da daliban makarantar firamare da ke unguwar Life-Camp a Abuja.

kungiyar da ke rajin ganin ana karance-karance da ake kira “Rainbow Book Club” da kungiyar UNESCO su ne suka shirya bikin a Abuja ranar Litinin din da ta gabata.

Yemi Osinbajo ya karanta wa daliban makarantar wani yanki na littafin tarihin Dokta Nnamdi Azikiwe wanda fitaccen marubuci Olajire Olanlokun ya rubuta.

Mataimakin shugaban kasa ya fara daga shafi na uku ya kare a shafi na 96 inda shugabar kungiyar Rainbow, Misis Kalanga ta rika yi wa daliban karin bayanin wuraren da Osinbajo ya karanta.

Daga bisani daliban sun yi wa mataimakin shugaban kasar tambayoyi kan cin hanci da rashawa da shirin gwamnati na bayar da tallafi da siyasa da kuma yadda ya gudanar da rayuwarsa inda shi kuma ya rika ba su amsa daya bayan daya.

Da yake jawabi, Yemi Osinbajo ya bukaci daliban su kara dagewa wajen yin karatu tare da baiwa ilimi muhimmanci.

A jawabinta, Shugabar kungiyar, Misis Koko Kalango ta bayyana cewa kungiyar ta yi shekaru tana wayar da kan jama’a kan muhimmancin ilimi da karatu.

“kungiyarmu ta dade tana aikin wayar da kan jama’a don su san muhimmancin karatu da ilimi a rayuwarsu. Don ta hanyar karatu ne kawai za ka samu ilimi”. Inji ta.

Ta bayyana cewa babban kalubalen da ake fuskanta shi ne na rashin sanin muhimmancin ilimi da karatu.

Amma ta dage a kan cewa idan gwamnati ta gina dakunan karatu sannan kuma iyaye suka tallafawa ’ya’yansu ta hanyar sayan kayan karatu babu shakka za a yi maganin matsalar.

A jawabinta, Darakta Janar na kungiyar majalisar dinkin duniya ta UNESCO, Mis Audrey Azoulay wacce jami’in gudanarwa na kungiyar Ifeanyi Ajaegbo ya wakilta ya ce kungiyar tana baiwa masu dab’i da rubuce-rubuce damar samun ’yancin cimma burinsu a rayuwa.

Da yake yin jawabin maraba, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya yaba wa mataimakin shugaban kasa kan yadda duk da hidimomin da ke gabansa ya halarci bikin.

Ya yi kira ga daliban su yi koyi da mataimakin shugaban kasa sannan kuma su rika karance-karance don samun ilimi mai inganci.

A nashi jawabin, Ministan Birnin Tarayya na Abuja, Malam Muhammadu Musa Bello wanda ya karfafa muhimmanci ilimi a rayuwa ya bukaci daliban su dage da karatu don zama shugabanni nagari a nan gaba.

Daga bisani  daliban sun baiwa mataimakin shugaban kasa babban kati wanda ke dauke da hotunansu da ke nuna taswirar kasar da suke a nahiyar duniya.

Mataimakin shugaban kasar ya yaba wa daliban da irin kokarin da suke yi na samun ilimi mai inganci.

Ya yi fatan daliban za su zama shugabannin na gari da Najeriya za ta yi alfahari da su.