Osinbajo ne ya kitsa sauke ni daga SGF, ADC ta sauya Atiku — Babachir

Babachir ya ce zai ci gaba da bayyana ra’ayinsa kan yadda al’amura suke tafiya a Najeriya.

Osinbajo ne ya kitsa sauke ni daga SGF, ADC ta sauya Atiku — Babachir

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar ADC tare da kare kansa daga sukar magoya bayan Atiku Abubakar.

Lawal, ya sanar da ficewarsa daga ADC a ranar Litinin, inda ya zargi jam’iyyar da watsi da dimokuraɗiyya da kuma kauce wa tsarin zaɓen fid-da-gwani domin amfanar da Atiku da na kusa da shi.

Ya ce an tauye haƙƙin wasu ’yan takara kuma an riga an tsara sakamakon zaɓen tun kafin a gudanar da shi.

Da yake mayar da martani kan sukar da ya fuskanta, Lawal ya ce ba ya damuwa da kalaman magoya bayan Atiku.

Haka kuma ya musanta zargin cewa an tsige shi daga muƙaminsa saboda almundahanar kuɗi.

“Zargin cewa an kore ni daga aiki saboda cin hanci ko rashawa ba gaskiya ba ne. Abin da ya faru wani shiri ne na musamman da aka yi domin a kore ni saboda kusancina da marigayi Shugaba Buhari,” in ji Lawal.

Tsohon sakataren ya ce wasu ’yan siyasa sun nuna rashin jin daɗi kan tasirinsa a gwamnati, lamarin da ya sa suka yi ƙoƙarin ganin an cire shi daga muƙaminsa.

“Majalisar Dattawa ta ba da shawarar a kore ni, amma da farko Shugaban Ƙasa ya yi watsi da shawarar. Daga baya kuma mataimakin shugaban ƙasa na lokacin ya ci gaba da matsa lamba har sai an sake gudanar da bincike wanda ya kai ga tsige ni daga muƙamin,” in ji shi.

Ko da yake bai ambaci suna kai-tsaye ba, Lawal ya yi zargin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, yana da hannu a tsige shi daga muƙaminsa.

Ya kuma ce daga baya EFCC ta gudanar da bincike kan lamarin, kuma kotu ta wanke shi bayan shaidu sun kasa danganta shi da wani laifi.

Lawal ya jaddada cewa babu wata almundahana da aka yi da kuɗin gwamnati, yana mai cewa an aiwatar da kwangilar da ake magana a kai yadda ya kamata.

Har ila yau, ya kare sukar da yake yi wa Atiku, yana mai cewa ’yan Najeriya suna da ’yancin tantance hali da ƙwarewar duk wanda ke neman zama shugaban ƙasa.

“Ina ganin ADC ya kamata ta maye gurbin Atiku da wani ɗan takara mafi cancanta idan har tana son samun damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027,” in ji Lawal.

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da bayyana ra’ayinsa kan batutuwan da yake ganin suna da muhimmanci ga Najeriya duk da sukar da yake fuskanta daga abokan hamayya da magoya bayan Atiku.