Osinbajo ya bude kamfanin shinkafa mafi girma a Afirka a Kebbi
Mukaddashin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bude masana’antar zazzabe shinkafa mafi girma a Nahiyar Afirka da aka gina ta a kan Naira biliyan 10 a garin Argungu da ke Jihar Kebbi. Da yake jawabi lokacin kakddamar da kamfanin ma suna WACOT Rice Mill, a ranar Talata da ta gabata, Farfesa Yemi Osinbajo ya nanata kudirin […]

Mukaddashin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bude masana’antar zazzabe shinkafa mafi girma a Nahiyar Afirka da aka gina ta a kan Naira biliyan 10 a garin Argungu da ke Jihar Kebbi.
Da yake jawabi lokacin kakddamar da kamfanin ma suna WACOT Rice Mill, a ranar Talata da ta gabata, Farfesa Yemi Osinbajo ya nanata kudirin Gwamnatin Tarayya na inganta harkokin noma a kasar nan, inda ya ce makomar Najeriya ta ta’allaka ne kacokam kan noma da ma’adinai.
Mukaddashin Shugaban kasar ya ce a sau da dama Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha nanata alfanun noma, inda yake karfafa cewa noma da ma’adinai za su taka rawar gani wajen habaka tattalin arzikin kasar nan.
Mukaddashin Shugaban ya bayyana cewa wannan kaddamarwar ta kasance wata gagarumar nasara da wannan gwamnatin ta cimma wajen karkatar da akalar tattalin arzikin kasar zuwa ga noma.
Farfesa Osinbajo ya kara da cewa sanya kudi kimanin Naira biliyan 10 a harkar a kasa da wata 12, ya nuna yadda kasar ke motsawa zuwa ga hanya madaidaiciya.
Ya cewa zuba jari a fannin noma da kamfanoni masu zaman kansu ke yi nuna goyon baya ga shirin samar da abinci da wadata shi a kasa da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta. Osinbajo ya yaba wa mutanen da suka zuba jari a kamfanin na WACOT, inda ya ce, hakan zai kawo ci gaba da bunkasa kamfanoni masu zaman kansu su shiga shirin bunkasa noman shinkafa da zazzabe ta a Najeriya.
Ya yi kira ga masu zuba jari su shiga harkokin noma domin samar da aikin yi ga jama’a musamman idan aka yi la’akari da yadda watsi da noma da harkokin ma’adanai suka haifar da asarar dimbin ayyuka a kasar nan.
Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana cewa kamfanin sarrafa shinkafar na WACOT ya samu ne a cikin shekara daya kacal, bayan da Shugaban kasa ya kaddamar da shirin bai wa manoma rance don noman rani a Jihar Kebbi. Ya kara da cewa kamfanin shinkafar na farko a jihar wato Labana yana nan haskawa yadda ya kamata, amma samuwar WACOT ya kara tabbatar da cewa zai taimaka hatta ga Gwamnatin Tarayya wajen dogaro da kai ta fuskar abinci.
Tun farko a jawabin, Babban Daraktan Kamfanin na WACOT, Mista Rahul Sabara ya ce Kamfanin WACOT shi ne kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a Afirka, inda ya ce kamfanin zai rika zazzabe shinkafa tan 400 a kullum da kuma tan dubu 120 a shekara. Kuma ya ce kamfanin shi ne irinsa na farko tun hawan wannan gwamnati gadon mulki, kuma sun tanadi manoma kimanin dubu 50 wadanda za su rika wadata kamfanin da shinkafar da yake bukata.