Ouattara ya sake lashe zaven Kwaddibuwa
A shekaranjiya Laraba ne aka sanar da Alassane Ouattara a matsayin zavavven Shugaban kasar Kwaddibuwa a karo na biyu. Hukumar zaven kasar ta ce Shugaba Ouattara ya yi nasara a zaven da a ka gudanar ranar Lahadi da kuri’u fiye da kashi 83 cikin 100 da aka kada.Babban abokin hamayyarsa shi ne tsohon Firaministan kasar, […]
A shekaranjiya Laraba ne aka sanar da Alassane Ouattara a matsayin zavavven Shugaban kasar Kwaddibuwa a karo na biyu.
Hukumar zaven kasar ta ce Shugaba Ouattara ya yi nasara a zaven da a ka gudanar ranar Lahadi da kuri’u fiye da kashi 83 cikin 100 da aka kada.
Babban abokin hamayyarsa shi ne tsohon Firaministan kasar, Pascal Affi N’Guessan, wanda ya samu kashi tara cikin 100 na kuri’un, kuma ya yi takara ne a karkashin jam’iyyar IPF ta tsohon Shugaba Laurent Gbagbo wanda Ouattara ya kayar da zaven shugaban kasar shekarar 2010.
’Yan takara na jam’iyyun hamayya da dama sun fice daga yakin neman zaben inda suka yi korafin cewa ba za a gudanar da zaven gaskiya ba.
Sai dai masu sa ido kan zaven sun ce sun gamsu da yadda zaven ya gudana.
Wannan dai shi ne babban zave na farko tun bayan zave mai zafi sosai da aka gudanar a kasar a shekarar 2010, wanda ya janyo varkewar yakin basasar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3,000.
A wani labarin kuma mai kama da wannan, a ranar Lahadin da ta gabata aka gudanar da zavuka a kasashen Tanzaniya da Polland da Guatemala da kuma Argentina, sai kasar Kongo Brazzaville wadda ta gudanar da kuri’ar raba-gardama kan bukatar shugaban ta neman wa’adi na uku.
Kodayake, zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai ga sanar da wanda ya samu nasara a zaven Tanzaniya ba, kuma ko a shekaranjiya Labara sai da aka soke zaven shugaban kasar da aka yi a yankin Zanzibar da ke kasar. Kuma aka ba da umarnin sake gudanar da sabo.
Amma a Kongo ’yan kasar fiye da kashi 90 cikin 100 ne suka amince da Shugaba Denis Sassou Nguesso ya tsaya takara a karo na uku. Har ila yau, a kasar Argentina ana sa ran zaven zai kai zuwa zagaye na biyu ne, wanda za a gudanar a watan gobe. Amma a kasar Polland ’yar adawar kasar, Beata Szydlo ce ta samu nasara. Hakazalika, wani mai wasan barkwanci mai suna, Jimmy Morales, shi aka bayyana a matsayin sabon shugaban kasar Guatemala, bayan kammala kidaya kuri’un da aka kada ranar Lahadin da ta wuce.
Har ila yau, a jibi Lahadi ne za gudanar da zaven shugaban kasa a kasar Turkiyya.