P-Skuare sun fitar albam din ‘Double Trouble’

Shahararrun mawakan Hip-Hop ’yan Najeriya Peter da Paul wadanda aka fi sani da P-Skuare sun fitar da sabon albam dinsu yau Juma’a mai taken ‘Double Trouble’Wakokin albam din sun hada da ‘Shekina’ da ‘MMS’ (Mugu Money Spender) da ‘Ejeajo wadda suka yi da mawakin gambara dan Amurka, T.I., sai  ‘Collabo’ wadda suka yi ta da […]

P-Skuare sun fitar albam din ‘Double Trouble’
P-Skuare sun fitar albam din ‘Double Trouble’

Shahararrun mawakan Hip-Hop ’yan Najeriya Peter da Paul wadanda aka fi sani da P-Skuare sun fitar da sabon albam dinsu yau Juma’a mai taken ‘Double Trouble’
Wakokin albam din sun hada da ‘Shekina’ da ‘MMS’ (Mugu Money Spender) da ‘Ejeajo wadda suka yi da mawakin gambara dan Amurka, T.I., sai  ‘Collabo’ wadda suka yi ta da Don Jazzy da ‘Enemy Solo’ wadda suka yi ta da  Awilo da kuma ‘Zombie’ wadda suka yi ta da Jermaine Jackson.
Masu sharhi sun ce wakokin za su kayatar da masu saurare, kuma sun zo da wani salo masu jan hankali da kuma motsa zuciya kamar yadda ake yi wa kauraye kidan gangi.
A cikin albam din akwai kidan taushin wakar ‘Testimony’ da ‘Personally’ da kuma ‘Alingo’.
Wannan shi ne albam din mawakan na shida, inda suka fitar da albam din da suka hada da ‘The Inbasion’ da ‘Get Skuared’ da ‘Danger’ da ‘Game Ober’ da sauransu.