P Skuare sun kayatar a Amurka da Kanada

Fitattun tagwayen mawakan Najeriya Paul da Peter da ake yi wa lakabin P Skuare sun kayatar a Amurka da Kanada.Mawakan sun gudanar da wake-wake da raye-raye na mako biyu, inda dubban masoya suka rika tafa musu hade da ihu da kuma tsalle.A yanzu mawakan sun kama hanyar zuwa kasar Habasha.Mawakan sun ce za su ci […]

P Skuare sun kayatar a Amurka da Kanada

P Square lokacin da suka sauka a AmurkaFitattun tagwayen mawakan Najeriya Paul da Peter da ake yi wa lakabin P Skuare sun kayatar a Amurka da Kanada.
Mawakan sun gudanar da wake-wake da raye-raye na mako biyu, inda dubban masoya suka rika tafa musu hade da ihu da kuma tsalle.
A yanzu mawakan sun kama hanyar zuwa kasar Habasha.
Mawakan sun ce za su ci gaba da rangadi a Karebiya da Nahiyar Turai  da Asiya, inda kuma za su kammala a Dubai a ranar 26 ga watan Disamba, 2013.
Yayin rangadin nasu a Amurka da Kanada sun yi wakokinsu a Dallas da Kalifoniya da Washington DC da kuma Montreal.
Sun bayyana jin dadinsu da irin tarbarsu da aka yi a Amurka da Kanada.
Paul ya ce: “Yadda aka karbe mu ya karfafa mana gwiwa, ya kuma ba mu karsashin ci gaba yin wakokin da za su sanya jama’a nishadi.