Ahmad Isa ne Gwarzon Ɗan Najeriya na 2024

Ahmad Isa ne Gwarzon Ɗan Najeriya na 2024
Ahmed Isah wanda aka fi sanni da 'Ordinary President'

Ahmad Isa ne Gwarzon Ɗan Najeriya na 2024, inji ma’abota shafukan Trust Radio

Abdulhadi Abubakar Umar

Ahmad Isa, wanda aka fi sani da Ordinary President, shi ne ɗan Najeriyar da ya fi kowa ƙoƙari wajen kawo sauyi a rayuwar al'umma a shekarar 2024.

Fitaccen ɗan jaridar ya samu wannan matsayi ne kamar yadda sakamakon wata ƙuri’a da masu bibiyar shafukan sadarwa na zamani na Trust Radio suka yi ya nuna.

“Trust Radio tasha ce da ta ƙuduri aniyar kawo sauyi a rayuwar ’yan Najeriya ta hanyar ba su damar bayyana abin da yake zuciyarsu da kuma samar musu labarai da bayanai na gaskiya da za su sauya rayuwarsu – wannan ne ya sa muka dacewar bai wa masu bibiyarmu damar fito da wani ɗan Najeriya wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan buri a 2024”, inji Shugaban tashar, Muhammad Kabir Muhammad.

Ahmad Isa ne dai ya samu kaso mafi tsoka na ƙuri’un da ma’abota shafukan na Trust Radio suka kaɗa a Facebook da X (Twitter a da) daga cikin mutum ukun da aka fitar.

Sauran mutum biyun su ne Fauziyya D. Sulaiman da Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan.

Ordinary President ɗin dai ya samu kashi 57.54 cikin 100 na ƙuri'un da masu bibiyar shafukan na Trust Radio suka kaɗa, yayin da Fauziyya D. Sulaiman ta zo a mataki na biyu da kashi 32.7, shi kuma VeryDarkMan ya take musu baya a mataki na uku da kashi 5.54 cikin 100.

Wanene Ahmad Isa ?

Ahmad Isa fitaccen ɗan jarida ne, mai fafutuka ne, kuma mai taimakon al’umma.

A shekarar 2024 ya taimaka wajen sauya rayuwar mutane da dama ta hanyar shirinsa na “Brekete Family”, wanda ake yadawa a rediyo da talabijin da ma kafofin sadarwa na zamani.

Ya saba taka muhimmiyar rawa wajen samar da kafa ga mutanen da ba su da wata hanyar miƙa kokensu don isar da saƙo zuwa inda ya dace.

Ya fara gabatar da shirin mai farin jini ne a shekarar 2009 a gidan rediyo na Kiss FM da ke Abuja.

Daga bisani ya koma gabatar da shi a gidan rediyo na Crowther Love FM, kafin ya kafa gidan rediyonsa na Human Rights Radio a Abuja, a shekarar 2017.

Sanadiyyar shirin na “Brekete Family”, ya fuskanci ƙalubale da dama, amma hakan bai hana shi ci gaba da aikinsa ba.

Sauyi a rayuwar al’umma

Ko a shekarar 2024, akwai mutane da yawa da Ordinary President ya fitarwa kitse a wuta, ta hanyar bankaɗo abubuwa da dama, har ta kai idon 'yan Najeriya da mahukunta ya kai wurin.

Wasu daga cikin abubuwan da ya yi a 2024 su ne:

Ruɗanin mutuwar mawaƙi MohBad

A farkon shekarar 2024, mahaifin matashin mawaƙin nan, Mohbad, wanda mutuwarsa ta zo da ruɗani, ya halarci shirin “Brekete Family”, inda ya buƙaci a bi masa haƙƙin kisan da ya yi zargi an yi wa ɗansa.

Taimak o ga wata uwar marayu

Ba za a manta da taimakon Naira Miliyan 1 da shirin “Brekete Family” ya tara wa wata mata wadda mijinta ya mutu ya bar ta da ’ya'ya, amma ɗan uwan mijin ya yi sama da faɗi da dukiyar marayun ba.

Sakin Seaman Abbas

Wani abu da ya ja hankalin jama'a game da tasirin Ahmad Isa a shekarar 2024, shi ne yadda wata mata da ake kira Husaina Haruna ta kai koke a kan yadda aka shafe shekaru shida ana tsare da mijinta Seaman Abbas Haruna, wanda ba ta san halin da yake ciki ba.

Matar, kamar yadda ta faɗa, ta bi duk hanyoyin da suka dace don ganin an saki mijin nata, amma abu ya gagara.

Zuwanta “Brekete Family” ya yi tasiri har ta kai Hedikwatar Tsaron Najeriya ta magantu kan batun, daga bisani kuma Rundunar Sojin Ruwa ta saki Seaman Abbas, tare da korar shi daga aiki.

Bai wa Hamdiyya Sidi Shariff aiki

Hamdiyya Sidi Sharif, wacce labarinta ya karaɗe gari saboda dambarwarta da Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta samu aiki a matsayin wakiliyar Human Rights Radio a Sakkwato, saboda a cewar Ahmad Isa hakan zai ƙara mata ƙaimi wajen tsage gaskiya komai ɗacinta.

Rayuwarsa ta bayan fage 

Ahmad Isa mutum ne da ba ya bayyana rayuwarsa ta bayan fage.

Amma ya tabbatar da yana da aure da ’ya'ya.

Kuma ya yi rayuwa a wurare daban-daban inda ake da al'adu da addinai daban-daban a Najeriya.