…Pakistan ta fara tattaunawar zaman lafiya da Taleban

Shugaba Nawaz Sherrif  na kasar Pakistan ya kaddamar kwamitin mutanen da za su yi tattaunawar zaman lafiya da ’yan tawayen Taleban.Wadanda za su wakilci gwamantin Pakistan a wajen tattaunawar da na ’yan Taleban sun gana a Talatar da ta gaba, inda suka tattauna yawan kashe-kashen mutane da ake yi. Sai dai ana tababar samun nasarar […]

…Pakistan ta fara tattaunawar zaman lafiya da Taleban
…Pakistan ta fara tattaunawar zaman lafiya da Taleban

Shugaba Nawaz Sherrif  na kasar Pakistan ya kaddamar kwamitin mutanen da za su yi tattaunawar zaman lafiya da ’yan tawayen Taleban.
Wadanda za su wakilci gwamantin Pakistan a wajen tattaunawar da na ’yan Taleban sun gana a Talatar da ta gaba, inda suka tattauna yawan kashe-kashen mutane da ake yi. Sai dai ana tababar samun nasarar masu shiga tsakanin.
Rukuni biyu na mutanen da Gwamna ta dora wa alhakin ganawa da ’yan kungiyar Tehreek-e- Taleban Pakistan (TTP), sun yi taro a birnin Islamabad, inda suka zayyana matakan da ya kamata a dauka a wajen tattaunawar.
Wannan al’amari ya bai a mutane mamaki, kan yadda Firayiminista Nawaz Sharif ya kafa gungun wadanda za su gana da ’yan tawayen, da ke yaki da gwamnatin tun daga shekarar 20007. Don a hasashen masu nazarin al’amura, an dauka zai kaddamar da mummunan hari a yankunan da ’yan Taleban ke da karfi a farkon wannan shekarar. Fiye da mutumn 110 suka mutu a hare-haren da aka kai cikin watan Janairun bana, kuma wadanda suka rasa rayukansu, mafi yawansu sojoji ne.
Masu sukar Gwmanatin Sharif na ganin ya kasa samun mafita daga tashe-tashen hankula, sannan kafafen yada labarai na nuni da cewa da wuya a samu nasara a tattaunawar da za a yi. Domin kungiyar Taleban ta nuna adawarta ga dimokuradiyya, inda gwamnati kuwa ta nuna cewa dole ne a tsayu kan kundin tsarin mulki. Jaridar kasar da ake wallafawa a cikin harshen Ingilishi, “The Nation,” ta yi labarinta mai taken “Tattaunawar zaman lafiya ta kusa tarwatsewa (“peace talks balloon will burst soon enough”.)