Pakistan ta kai hare-haren sama a Afghanistan

Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce, hare-haren sun kashe mutane 13, ciki har da yara 11.

Pakistan ta kai hare-haren sama a Afghanistan

Kasar Pakistan ta ƙaddamar da hare-haren sama masu muni a kan iyakarta da Afghanistan, lamarin da ya kawo ƙarshen zaman lafiya na watanni da aka samu a yankin da ke fama da rikici.

Ministan Yaɗa labaran Pakistan, Attaullah Tarar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa, an lalata wurare huɗu a wani hari da aka yi cikin tsari, wanda ya kashe ’yan bindiga 26.

Amma Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce, hare-haren sun kashe mutane 13, ciki har da yara 11.

Pakistan ta daɗe tana zargin Afghanistan da bai wa ’yan ta’adda mafaka, domin kai hare-hare a cikin ƙasarta, zargin da Gwamnatin Taliban ke ci gaba da musantawa.

Wannan sabon rikici shi ne na farko tun watan Fabrairu, lokacin da ƙazamin faɗa a kan iyaka ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane.

ƙasashen biyu sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoban bara, bayan makonni na rikice-rikice masu muni.

Attaullah Tarar ya ce, hare-haren sun zo ne a matsayin martani ga “sababbin hare-haren ta’addanci a Pakistan,” inda aka kai farmaki kan wuraren ɓuya da horar da ’yan bindiga da kuma wuraren ajiye makamai a yankin iyakar.

Tun bayan ƙazamin rikicin da ya faru a ƙarshen watan Fabrairu, akan samu arangama lokaci-lokaci, yayin da shugabannin duniya ke kira ga ƙasashen biyu da su dakatar da rikicin tare da rungumar zaman lafiya.