Pakistan ta kama Amin Ul-Haq wani na kusa da Osama Bin Laden

Amin Ul-Haq na daya daga cikin mutanen da bayan kisan Usama Bin Laden ke kokarin sake farfadowa

Pakistan ta kama Amin Ul-Haq wani na kusa da Osama Bin Laden

Ayman al-Zawahri da Osama Bn Ladin

Hukumomin Pakistan sun ce a yau Juma’a sun kama wani na kusa da Usama Bin Laden wanda ya kafa kungiyar Al-Qaeda kuma wanda ya jagoranci harin 11 ga Satumba.

Jami’an yaki da ta’addanci a lardin Punjab mafi yawan jama’a sun kai farmaki kan Amin Ul-Haq a birnin Gujrat.

Sanarwar da ma’aikatar yaki da ta’addanci ta Punjab ta fitar ta ce  samamen da suka kai wanda ya kai su ga kama Amin Ul-Haq wata babbar nasara ce a kokarin da ake na yaki da ta’addanci a wannan kasa ta Pakistan da ma duniya baki daya.

Kasashe irinsu Amurka da Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya sun saka shi a matsayin dan kungiyar Al-Qaeda da Bin Laden.

Osama bin Laden
Osama bin Laden Reuters

Shugaban sashin yaki da ta’addanci na Punjab Usman Akram Gonadal ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai.

Amin Ul-Haq na daya daga cikin mutanen da bayan kisan Usama Bin Laden ke kokarin sake farfadowa da ayukan wannan kungiya bayan janyewar dakarun NATO daga yammacin Afghanistan.

Amin Ul-Haq ya ziyarci Afganistan a watan Agusta kuma ya fara kokarin sake tsara kungiyar ta Al-Qaeda.

 Sojojin Amurka da ke samun goyon bayan kungiyar NATO sun hambarar da gwamnatin Taliban ta farko a shekara ta 2001 saboda kin mika mayakan Al-Qaeda da suka kai harin 11 ga Satumba.

Daga baya an gano Bin Laden yana zaune a Pakistan kuma an harbe shi a wani harin da Amurka ta kai da daddare a shekarar 2011.

A shekarar 2021 ne kungiyar Taliban ta karbe mulki a Afganistan, inda ta kori gwamnatin da ke samun goyon bayan kasashen waje bayan shafe shekaru 20 tana yakar sojojin Amurka da na NATO.

Tuni dai mayakan suka yi kaca-kaca a kan iyakar Pakistan, inda Islamabad ke zargin mahukuntan Kabul da gazawa wajen kawar da kungiyoyin da ke samun mafaka a kasar Afganistan yayin da suke shirin kai hari kan Pakistan.

Gwamnatin Taliban ta dage cewa ba za ta kyale kayyakin mayakan na kasashen waje su yi aiki daga Afganistan ba, amma dangantakar Islamabad da Kabul ta yi tsami kan batun.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos