Pakistan za ta gina masallaci na uku mafi girma a duniya
A ranar Talatar da ta gabata ne aka dasa harsashin ginin masallaci na uku mafi girma a duniya a garin Bahria kusa da birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda idan aka kammala aikinsa zai bai wa masallata 25,000 damar gudanar da ayyukan ibada lokaci guda. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, wani dattijo ne mai shekara […]
A ranar Talatar da ta gabata ne aka dasa harsashin ginin masallaci na uku mafi girma a duniya a garin Bahria kusa da birnin Karachi na kasar Pakistan, wanda idan aka kammala aikinsa zai bai wa masallata 25,000 damar gudanar da ayyukan ibada lokaci guda.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, wani dattijo ne mai shekara 73 ne ya aza harsashin ginin sabon masallacin saboda shi ya fi sauran leburori da za su yi aikin ginin tsufa. Kuma an ruwaito cewa idan aka kammala aikinsa, masallacin zai kafa tarihi a fuska biyu, da farko shi zai zama masallaci mafi girma a kasar. Hakazalika, na uku mafi girma a duniya.
Masallaci da ake fatan kammala gininsa a cikin shekara biyar, za a mai hasumiyya guda daya ne, wadda tsawonta zai kai kafa 325. Kuma zai kunshi Jami’ar Musulunci da dakin Karatu da Cibiyar Binciken addinin Musulunci da kuma gidan tarihi.