Pantami da Amaechi za su bayyana a gaban majalisa
Za su amsa tambayoyi kan karbar rancen Dala miliyan 500 da sauransu
Isa Ali Pantami, Ministan Sadarwan Najeriya. (Tsohuwar ajiya).
Majalisar Wakilai ta gayyaci Ministan Fasahar Sadarwa Isa Ali Pantami da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi kan rancen Dala miliyan 500 na aiki jirgin kasa da sauransu a fadin Najeriya.
Majalisar ta kuma gayyaci Ministar Kudi Zainab Ahmed Darekta Janar na Ofishin Kula da Basuka (DMO) Patience Oniha su zo tare da su domin bayani a kan rancen daga bankin shige da fice na kasar China.
Shugaban Kwamitin Sulhu da Tsare-tsare na Majalisar, Ossai Nicholas a ranar Talata ya bukaci ministocin su hallara ranar 17 ga watan Agusta.
Ossai Nicholas ya bukaci dukkansu da a kawo dukkan takardun yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da kamfanin CCECC na kasar China kan aikin jirgin kasa na Abuja-Kaduna, Lagos-Ibadan, Ibadan-Kaduna da kuma Kaduna-Kano.