Pantami ya ba Airtel kwana uku ya gyara matsalar sadarwa

Gwamnatin Tarayya ta ba wa kamfanin sadarwa na Airtel wa’adin kwanaki uku ya gyara hanyoyin sadarwarsa tare da warware matsalolin jama’ar da ke hulda da shi. Ministan  Sadarwa da Tattalin Arzikin, Dakta Isa Ali Pantami ya sanar da haka ta shafinsa na Twitter. Airtel ya samar da layin waya don yaki da mace-macen mata NCC […]

Pantami ya ba Airtel kwana uku ya gyara matsalar sadarwa

Isa Ali Pantami, Ministan Sadarwan Najeriya. (Tsohuwar ajiya).

Gwamnatin Tarayya ta ba wa kamfanin sadarwa na Airtel wa’adin kwanaki uku ya gyara hanyoyin sadarwarsa tare da warware matsalolin jama’ar da ke hulda da shi.

Ministan  Sadarwa da Tattalin Arzikin, Dakta Isa Ali Pantami ya sanar da haka ta shafinsa na Twitter.

Pantami ya umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) umarnin bincikar lamarin inda ya ce “na samu korafe-korafe a kan kamfanin Airtel kuma ina so ku yi bincike tare da gabatar min da sakamakon binciken cikin kwanaki 3 sannan a kuma a tabbatar an warware matsalolin da abokan hulda da kamfanin ke fuskanta”, inji Pantami.

A cikin karshen makon jiya ne mutane da dama suka shiga bayyana korafinsu kan Airtel musamman a Twitter tare da neman dauki daga Ministan.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa