Pantami ya cancanci zama Farfesa — ASUU
Kwamitin ya ce ya gano an bi dukkan ka’idoji kafin tabbatar masa da mukamin.
Wani kwamiti da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta kafa don binciken matsayin Farfesa da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Owerri ta ba Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami ya tabbatar da sahihancin hakan.
Kwamitin, ya ce ya gano babu wata cuwa-cuwa a bayar da matsayin na Farfesan ga Dokta Isah Ali Pantami.
- Kasa ta rufta da mutum 25 masu hakar zinari a Maradi
- Masu garkuwa da mutane sun bukaci ‘Maltina’ a matsayin fansa
ASUU dai ta kafa kwamitin ne bayan cece-kucen da ya barke kan mukamin da jami’ar ta Owerri ta ba Ministan don binciken gaskiyar al’amarin daga wurin Hukumar Gudanarwar Jami’ar.
Sai dai bayan kammala binciken da ASUU ta yi, ta gano babu wata cuwa-cuwa a wajen tabbatar da mukamin.
Kwamitin ya kara da cewa an cika dukkan wasu sharudda da ka’idoji da Hukumar Makarantar ta tanada wajen bayar da mukamin.
Baya ga haka, kwamitin ya tabbatar da makalar da shi Ministan ya rubuta tare da wallafa ta a Bangaren Koyar da Ilimin Fashar Sadarwa da Tsaro ta Intanet na Makarantar, wanda bayan duba cancantar takardar, ya sa aka bashi matsayin na Farfesa.
Shugaban Kwamitin, Farfesa M. S. Nwakaudu tare da sauran mambobinsa hudu, duk sun rattaba hannu inda suka ce a iya binciken da ya kamata a yi, sun gano babu wata cuwa-cuwa wajen bayar da mukamin.
Daga karshe kwamitin ya bayar da shawarar a dauki mataki kan duk wanda ya yi yunkurin bata sunan Hukumar Gudanarwar Makarantar a kan lamarin.