Pantami ya yi Allah-wadai da kisan masallata a Katsina
Pantami ya ce jami’an tsaro za su iya amfani da fasahar zamani wajen gano inda masu laifin suke.
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi Allah-wadai da kisan masallata da ’yan bindiga suka yi a wani masallaci da ke Malumfashi, a Jihar Katsina.
Harin ya faru ne a ranar Talata lokacin da mutane ke sallar Asubah, inda aka kashe aƙalla mutane 27, sannan aka jikkata wasu da dama.
- Diyyar sansanin Boko Haram da Gwamnatin Tarayya ta ba mu bai isa ba — Gwamnatin Gombe
- Hajjin 2025: EFCC ta kama manyan jami’an NAHCON kan zargin almundahanar kuɗi
Shugabannin al’umma da jami’an asibiti ne suka tabbatar da harin.
Farfesa Pantami, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, al’ummar Unguwan Mantau da kuma ɗaukacin mutanen Katsina.
Ya bayyana cewa waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki “sun fi dabbobi muni,” domin sun kashe mutane ne a yayin suke ibada.
Ya buƙaci hukumomin tsaro su ɗauki mataki mai tsauri kan ’yan ta’addan, tare da amfani da fasahar zamani wajen gano su.
A cewarsa, jami’an tsaro na iya amfani da bayanan wayar hannu, hasashen hasumiyoyin sadarwa, da tsarin GPS don gano masu laifin.
Ya ce ya daɗe yana bayar da wannan shawara tsawon shekaru shida da suka wuce.
Pantami, ya yi addu’a Allah Ya karɓi shahadar waɗanda aka kashe, Ya kuma bai wa iyalansu haƙuri da juriya.
Haka kuma ya yi addu’ar zaman lafiya da tsaro a Najeriya baki ɗaya.