Patience Ozokor ta fara fim din Hausa

Fitacciyar jarumar fina-finan Kudancin Najeriya (Nollywood) Patience Ozokor da aka fi sani da Mama G ta fara fitowa a fina-finan Hausa.Ta fito a cikin fim din ‘Hassana da Hussaina’ wanda Kamfanin Faidhat Production da ke Kano ya shirya.An shafe kwana goma yayin daukar fim din a Kaduna da kuma Abuja.Jarumar ta bayyana wa Aminiya jin […]

Patience Ozokor ta fara fim din Hausa
Patience Ozokor ta fara fim din Hausa

Fitacciyar jarumar fina-finan Kudancin Najeriya (Nollywood) Patience Ozokor da aka fi sani da Mama G ta fara fitowa a fina-finan Hausa.
Ta fito a cikin fim din ‘Hassana da Hussaina’ wanda Kamfanin Faidhat Production da ke Kano ya shirya.
An shafe kwana goma yayin daukar fim din a Kaduna da kuma Abuja.
Jarumar ta bayyana wa Aminiya jin dadinta sakamakon gayyatar ta da masu shirin fim din Hausa suka yi.
“Na ji dadi sosai, wannan ya nuna mini cewa an karbi dukkan ayyukan da nake yi a Najeriya ba wai wani bangare ba kawai.” Inji jarumar.
Ta ce wannan fim din da ta yi ya nuna mata yadda al’adar Hausawa take, ta kuma fahimci Hausawa suna da yakana da karimci da kuma rashin nuna bambancin yare ko addini.
Fim din ‘Hassana da Hussaina’ labari ne a kan Hassana (Saratu Gidado) da kuma Hussaina (Patience Ozorkor) da kuma mahaifinsu Uche (Baban Chinedu). A fim din an nuna yadda mahaifinsu yake matukar son kudi, wanda ya sanya bai damu ya san halin mutum ba, matukar yana da kudi to zai iya aura masa ’ya’yansa ba tare da tunanin me zai je ya zo ba.
Akwai Hassan (Rabilu Musa Ibro) da Hussaini (Suleiman Bosho) ’ya’yan Alhaji Ibrahim (Magaji Mijinyawa) wanda yake tsohon soja ne, inda suka fitini kowa, mahaifinsu ba shi da wani buri face su yi aure.  
Wata rana Hassan da Hussaini sun fita yawon shakatawa sai suka hadu da Hassana da Hussaina, aka kuma kulla soyayya. Sai bayan an yi aure ne sai suka fahimci sun yi aure kamar 30, inda Hassana take da babban da, ita kuma Hussaina take da ’ya’ya ’yan wada.
Bayan an yi auren ne gida ya rikice wadanni suka addabi Hassan, haka kuma suka addabi Hussaina.
Furodusan fim din Abba Miko Yakasai ya ce duk da cewa fim din barkwanci ne, amma yana dauke da darussa masu yawa da suka hada da: Illar da ke cikin yin aure ba tare da bincike ba, illar neman aure a gidan da babu tarbiyya. Shawagaba ’ya’ya da iyaye suke yi.
Kamfani: Faidhat Production. Furodusa: Abba Miko Yakasai, Darakta: Hassan Giggs.