Paul Biya ya sauya jami’an tsaron fadar shi bayan juyin mulkin Gabon
Dai dai lokacin da juyin mulkin Soji ke ci gaba da bazuwa a kasashen Afrika, rahotanni daga Kamaru na cewa shugaban kasar Paul Biya ya yi garambawul ga majalisar tsaronsa.
Dai dai lokacin da juyin mulkin Soji ke ci gaba da bazuwa a kasashen Afrika, rahotanni daga Kamaru na cewa shugaban kasar Paul Biya ya yi garambawul ga majalisar tsaronsa.
Kamar yadda wata majiyar tsaro ta tabbatar, tun a yammacin jiya Laraba, shugaba Biya mai shekaru 90 ya sauya dukkanin masu tsaron lafiyarsa.
A cewar bayanai cikin jami’an tsaron da shugaba Paul Biya ya yi garambawul ya kunshi ilahirin wadanda ke bayar da kariya ga fadar shugaban kasa da suka kunshi Sojin sama da na ruwa da kuma ‘yan sandan.
Biya wanda ya haura shekaru 40 ya na mulkin kasar ta tsakiyar Afrika, ya hau karagar mulki ne tun a shekarar 1982, inda zarge-zargen take hakkin dan adam suka dabaibaye gwamnatinsa.
Paul Biya na sahun shugabannin Afrika mafiya dadewa a karagar mulki haka zalika mafiya tsufa lura da yadda korafe-korafe suka yi yawa kan lafiyar shi.
Wannan mataki na Biya dai na matsayin cikakkiyar kariya don kaucewa juyin mulkin da jami’an tsaron fadar shugaban kasa suka jagoranta a kasashen Nijar da Gabon.