PCNI ta kai ziyara bangaren wadanda rikici ya shafa a Asibitin kasa na Abuja
A kokarin da take yi wajen samar da lafiya mai inganci, Kwamitin Shugaban kasa kan sake gina Arewa Maso Gabas (PCNI) ya ziyarci bangaren wadanda rikici ya shafa a babban asibitin kasa a Birnin tarayya Abuja a ranar 20 ga watan Nuwamba 2017. Mataimakin shugaban Kwamitin, Tijjani M. Tumsah ya yi tsokaci a kan bukatar […]
A kokarin da take yi wajen samar da lafiya mai inganci, Kwamitin Shugaban kasa kan sake gina Arewa Maso Gabas (PCNI) ya ziyarci bangaren wadanda rikici ya shafa a babban asibitin kasa a Birnin tarayya Abuja a ranar 20 ga watan Nuwamba 2017.
Mataimakin shugaban Kwamitin, Tijjani M. Tumsah ya yi tsokaci a kan bukatar a samar da kiwon lafiya mai inganci a yankin, ganin cewa Maleriya, kwalara, ciwon suga da tamowa sun yi wa yankin katutu.
Mr. Tumsah wanda ya ga yadda ake horar da ma’aikatan da ke kula da marasa lafiya a asibitin kasa na Abuja wanda Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka ta turo jami’anta don su horar, ya nuna gamsuwarsa da irin na’urorin zamanin da ya ga ana amfani da su a wajen horarwar. Na’urorin sun hada da na gwajin numfashi da na bugun zuciya da sauransu.
Shugaban Tawagar ma’aikatan kiwon lafiya na Jami’ar Johns Hopkins ta Amurka, John B. Sampson, ya yi bayanin muhimmancin amfani da mutun-mutumin wajen horar da ma’aikatan asibiti don yin hakan yana rage hadarin amfani da dan Adam a horarwa a wajen yin fida da sauran gwaje-gwaje.
Ya ce hakan zai ba daliban koyon aikin asibiti damar kwarewa a bangaren binciken da ya shafi yin numfashi (Cardio-Pulmonary Resusciation (CPR), da bangaren sanya jariri a kwalba (Endotracheal incubatioin, da na gwaje-gwajen jini da kuma na yadda yakamata a rika rubutawa marasa lafiya magani musamman wadanda suka samu matsalar tabin hankali da ta kuna da sauransu.
Taken taron shi ne: “Matakan da suka kamata a bi idan bala’I ya auku” ya samu halartar ma’aikatan kula da lafiya daga wasu kasashe na Nahiyar Afirka.