PCNI ya yi hadin gwiwa da hukumomin UNDP da UNHCR don bayar da kariya ga masu komawa yankin Arewa maso Gabas

Tun daga ranakun 12 zuwa 13 ga Yulin 2017 Kwamitin shugaban kasa kan inganta yankin Arewa maso Gabas (PCNI) da Hukumar bunkasa ci gaban al’umma (UNDP) da Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya (UNHCR) sun shirya bita kan  tabbatar da samun sauki ga al’ummomin Arewa maso Gabas.    Jigon taron shi […]

PCNI ya yi hadin gwiwa da hukumomin UNDP da UNHCR don bayar da kariya ga masu komawa yankin Arewa maso Gabas

Tun daga ranakun 12 zuwa 13 ga Yulin 2017 Kwamitin shugaban kasa kan inganta yankin Arewa maso Gabas (PCNI) da Hukumar bunkasa ci gaban al’umma (UNDP) da Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya (UNHCR) sun shirya bita kan  tabbatar da samun sauki ga al’ummomin Arewa maso Gabas.    Jigon taron shi ne yadda za aiwatar da dabarun kariya da dawo da mazauna tare da farfado da yankin. A lokacin gudanar da bitar, mahalarta sun tattauna kan matakan warware matsaloli masu dorewa don  fuskantar kalubalen da suka addabi al’umma a yankin, musamman farfado da hanyoyin neman abinci da samar da kayan more jin dadin rayuwa.

A jawabinsa, Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI, Mista Tijjani Tumsah, wanda ya wakilci shugaba, Laftanar Janar T.Y danjuma (mai ritaya) ya yi nuni ne da muhimmancin kariya da dawowar wadanda yakin ya kora daga garuruwansu a kashin kansu, inda ya bijiro da muhimman al’amura masu alaka da juna, wato “kariya ga al’umma da kariyar masu fafutikar gyara, ta yadda za a saukaka wa al’ummomi da tallafi a harkar neman abincinsu.”

Ya yi nuni ga wani karamin  kwamiti da ke karkashin PCNI da aka dora wa alhakin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da daidaituwar al’amura, a karkashin Babban mai bayar da shawara kan  harkokin tsaron kasa (NSA) da Kwamandan rundunar da take tafiyar da yankin mai dimbin muhimmanci da ake da shi a kwamitin  PCNI. Masu bayar da tallafi da abokan hadin gwiwa, a cewarsa, sun hadu kan yadda za a cimma manufofi. Mista Tumsah ya ce kwamitin PCNI a halin yanzu ya mayar da hankali ne kacokan kan farfado da ayyukan hukuma a yankunan da al’amura suka sukurkurce, don haka ya yi alkawarin PCNI zai jajirce wajen bunkasa dabarun hadin gwiwa tare da daukacin masu ruwa da tsaki ta yadda za a samu kariya da saukin dawowar wadanda yakin ya kora daga garuruwan a kashin kansu.