PCNI za ta juya akalarta daga ayyukan jinkai zuwa na farfado da tattalin arziki
A ranar Talata 17 ga watan Oktoba ne PCNI ta gabatar da taronta na wata-wata karo na hudu. Taron ya hada duk masu ruwa da tsaki a harkar PCNI da suka hada da jihohin da suke taimakawa daidaikun mutane a harkar ayyukan jinkai da samar da tallafin cigaba a yankin Arewa maso Gabas, kuma an […]
A ranar Talata 17 ga watan Oktoba ne PCNI ta gabatar da taronta na wata-wata karo na hudu. Taron ya hada duk masu ruwa da tsaki a harkar PCNI da suka hada da jihohin da suke taimakawa daidaikun mutane a harkar ayyukan jinkai da samar da tallafin cigaba a yankin Arewa maso Gabas, kuma an yi taron ne a Otel din Sandralia da ke Jabi, Abuja.
Taken taron shi ne “Yadda za a sauya daga ayyukan jinkai zuwa na farfado da tattalin arziki mai daurewa,” makasudin wannan taron shi ne yadda za a canza akalar PCNI daga ayyukan jin kai da bayar da agajin gaggawa zuwa yadda za a farfado arziki mai daurewa. Wannan manufar na da amfani matuka ganin yadda sojoji ke ci gaba da kwato garuruwa daga hannun Boko Haram, kuma garuruwan ke bukatar komawa hannun farar hula da kuma dawowar wadanda suka bar garuruwan.
A jawabinsa, Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI, Tijjani M. Tumsah, ya ce canza akalar na da matukar muhimmanci “saboda a dawo da harkar kasuwanci, samar da abinci da tsaron abincin, da rage radadin talauci a shekaru masu zuwa.” Sannan ya bukaci ma’aikatun gwamnati, da bangarorin gwamnatin, da kuma wadanda suke bayar da gudunmuwa da su mayar da farfado da tattalin arziki babbar manufar su na badi, domin wannan ita ce hanya da mutanen Arewa maso Gabas za su samu “ci gaba kuma su kula da kansu.” Da yake bayanin kan yadda za a yi a samu nasara, Mista Tumsah ya tabbatar da cewa harkar noma ce babbar hanyar da za ta taimaka wajen farfado da yankin, sannan ya bukaci a mayar da hankali a bangaren domin mutane su daina jiran kayyakin jinkai.
Ya kara da cewa “jihohin da suke taimakawa, da daidaikun mutane da suke taimakawa, da kuma Kudin Tallafin na (bSF) sun fara mayar da hankali kan noma baya ga tallafin jinkai.” Sannan ya ce wannan zabin ne ya kamata ya zama abu mafi muhimmanci a yankin Arewa maso Gabas a shekaru masu zuwa. “ Kuma yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yaki da cin hanci da rashawa ya rataya ne kan yadda muka yi kokari wajen sa mutane su koma gona cikin sauri saboda yadda aka samu tsaro a yankin,” inji mataimakin shugaban. “Ayyukanmu na farfado da tattalin arziki na garuruwan da aka kwato zai taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen gyara garuruwan, tabbatar da su da rage talauci.”
Wadanda suka halarci taron sun hada da masu taimakawa wajen samar da cigaba daban daban, gwamnatoci da masu zaman kansu, kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma mambobin PCNI.