PDM za ta kafa gwamnati a Yobe a 2015 – Baba Ajiya
Sabuwar Jam’iyyar PDM a Jihar Yobe ta ce a halin yanzu tana nan tana shirin karbar ragamar jagorancin jihar daga gwamnati mai ci ta sabuwar Jam’iyyar APC.Shugaban Jam’iyyar PDM a jihar Alhaji Idris Baba Ajiya ne ya bayyana haka a tattaunwarsa da Aminiya a Damaturu, inda ya ce, don a tabbatar da kudirinsa na karbe […]
Sabuwar Jam’iyyar PDM a Jihar Yobe ta ce a halin yanzu tana nan tana shirin karbar ragamar jagorancin jihar daga gwamnati mai ci ta sabuwar Jam’iyyar APC.
Shugaban Jam’iyyar PDM a jihar Alhaji Idris Baba Ajiya ne ya bayyana haka a tattaunwarsa da Aminiya a Damaturu, inda ya ce, don a tabbatar da kudirinsa na karbe jagorancin jihar daga hannun gwamnati mai ci yanzu haka sun bude ofisoshin jam’iyyarsu a dukan kananan hukumomin jihar 17 tare da kokarin kai ziyara a yankunan don ganawa da magoya bayanta kan yadda za su ci zaben da ke tafe walau na kananan hukumomi ko gama-gari.
Ya ce a shirye suke su shiga zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a watan gobe idan aka sanar musu a kan lokaci tare da ba su takardun cikawa don shiga zaben.
Shugaban ya ce babu laifi kan sake sanya dokar ta-baci a jihar in an sa dokar ce da manufar tabbatar da zaman lafiya, domin sai da zaman lafiya ne za a gudanar da kowace harka da ta shafi rayuwa.
Ya roki gwamnatin jihar ta sassauta tsananin da ke tare da dokar musammnan kara lokacin walwala don al’umma na cikin mawuyacin hali ta yadda hatta abin da za su ciyar da kansu ke gagararsu.