PDP: Ba a bari a kwashe duk
Alhaji Adamu Mu’azu, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi ne babban shugaban jam’iyyar PDP na takwas da aka nada bayan tsohon shugabanta, Alhaji Bamanga Tukur ya ga haza, ya ajiye kwallon mangwaro don ya huta da kudajen da suka buwaye shi, har mulkinsa na watanni ashirin da biyu ya kasa yin armashi. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar […]
Alhaji Adamu Mu’azu, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi ne babban shugaban jam’iyyar PDP na takwas da aka nada bayan tsohon shugabanta, Alhaji Bamanga Tukur ya ga haza, ya ajiye kwallon mangwaro don ya huta da kudajen da suka buwaye shi, har mulkinsa na watanni ashirin da biyu ya kasa yin armashi. Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar na ganin cewa hakan shi ne mafita daga matsalolin da suka kame kurwarta, suka hana ta yin tasiri a gwamnatance; wasu kuma na ganin cewa da sauran rina a kaba, domin kuwa wannan ba ita ce hanyar kai wa ga makurar al’amuran da ke wahalar da ita ba. Daga cikin shugabannin jam’iyyar da suka gabata guda daya ne daga cikinsu, watau Kanar Ahmadu Ali ya wanye lafiya, ya fita da fitarsa, sauran duk haka nan aka yi ta hankada keyarsu, suna sauka daga kujerar shugabanci ba girma ba arziki. Akwai wani ma, Cif Nwodo wanda aka tursasa sauka daga kujerarsa a filin da ake zabe fitar da dan takara a shekarar 2011, yayin da aka ba shi alkalami da takarda ya kattabta murabus nan take, ko kuma ya gamu da gamonsa.
Irin abin da faru ga Alhaji Bamanga Tukur ke nan, wanda Shugaba Goodluck Jonathan ya daurewa gindi a watan Maris 2012 har aka dora shi kan kujerar mulkin jam’iyyar bayan an yi wa sauran ‘ya’yanta burum-burum a babban taron kasa na jam’iyyar har ta kai an yi dauki-dora wacce daga bisani ta zame tarin da ya tayarwa jam’iyya da aman da ya kawar da wasu shugabannin da aka zaba, aka kuma bayan kusan shekara guda aka sake zaben sabbi. Amma duk da haka nan kurar da aka rigaya aka tayar ta gawurta, ta zame kakkarfar guguwar da ta girgiza jam’iyyar, ta kasa zaune, ta kasa tsaye, har sai da ta kai wasu gwamnoni da ‘yan majalisa sun yi kaura zuwa shekar jam’iyyar adawa, kuma duk da haka nan tsuguni-tashi ba ta kare ba.
Kafin akai ga kumbuya-kumbuyar zaben Bamanga a matsayin shugaban jam’iyyar a 2012 sai da aka yi zaben fitar da gwani na shiyyar Arewa-maso Gabas inda ya fafata da wasu fitattun ‘yan siyasa, zarata, gogaggu, masu jini a jika, kuma kuri’u biyu kacal ya samu, Alhaji Adamu Mu’azu ya samu kuri’a guda, Alhaji Babayo kuma ya samu kuri’u 14. Amma da yake a Najeriya ba a son gaskiya sai aka biye wa son zuciya sai aka fitar da sunan Bamanga Tukur a matsayin dan takara daga shiyyar Arewa-maso-Gabas, aka murda, aka coga masa ya haye a babban taron kasa na jam’iyyar, inda ya zame shugabanta duk da tsananin hamayyar da aka yi ta nunawa.
An yi haka ne kuwa don a share wa Shugaba Goodluck Jonathan hanyar sake tsayawa takara a shekarar 2015, kuma da yake a lokacin suna dasawa da gwamnonin jihohi babu wata matsala game da haka. Gwamnoni sun amince, kuma duk abin da suka yarda da shi babu wani dan da jam’iyyar PDP ta haifa da ya isa ya muzanta, haka nan duk abin da suka haramta ba wani mai halastawa, haka nan za a hakura a bi ra’ayinsu in ana so a zauna lafiya. To ko a wannan karon ma abin da ya faru ke nan. Gwamnonin jam’iyyar ne suka fitar da sunan Ahmed Mu’azu duk kuwa da cewa suna sane da irin hayagagar da aka sha yi a kansa game da wasu makudan kudaden da ake zargin sun salwanta a hanunsa sa’ilin da ya shekara takwas yana damawa a matsayin Gwamnan Jihar Bauchi, da kuma yadda aka yi ta kai ruwa rana sa’ilin da Shugaba Jonathan ke son nada shi shugaban Hukumar Fanshon Ma’aikata, PENCOM, ya kuma yi nasarar yin haka tare da goyon bayan majalisar kasa.
An dai rigaya an rantsar da Adamu Mu’azu kan wannan mukamin, saura kuma a jira abin da zai biyo baya kafin lokacin da za a yi babban taron jam’iyyar, a kuma dakaci abin da zai haifar. Ta ko ina dai aka dubi yadda gwamnoni suka wanke Adamu Mu’azu, suka rufa shi a matsayin sabon angon jam’iyyar PDP, uwarta kuma tana ji, tana gani, ba ta ce hakan ya yi, ko kuma bai dace ba, sai a ce akwai manya-manyan ayyuka da ke gabansa, a kuma yi tambayar cewa ko wadancan gwamnonin da suka zame ‘ya’yan agwagwi masu wucewa gaban uwarsu, har suka daure wa Adamu Mu’azu gindi za su iya taimakonsa wajen sauke kayan da ke kansa don kar wuyansa ya dankare?
A yanzu dai Adamu Mu’azu ya gaji jam’iyyar da kowa ke ganin ta fatattake, ta wargaje, ta rasa kyakkyawar alkibla. To, wace irin allura ko basilla zai yi amfani da ita wajen dinke barakar da ke kara tabewa a kullum a cikin jam’iyyar? Akwai dabarar da zai yi don shawo kan ‘ya’yan jam’iyyar da son zuciya ta sa suka fandare, kowa ya kama gabansa? Anya kuwa zai iya magance matsalolin rashawa da cin hanci da ha’inci da rashin mutunci da suka dabaibaye jam’iyyar, suka hanata karsashi? Kuma akwai alamun zai iya tsira da mutuncinsa kafin zaben 2015; ko kuwa shi ma zai shiga tasku ne irin na shugabannin da suka gabace shi? Ba makawa talakawa za su ci gaba da yi masa addu’ar samun nasara domin zaman lafiyar jam’iyyar PDP shi ne kwanciyar hankalinsu, amma sai dai ya kamata ya san cewa shugabannin jam’iyyar da suka gabace shi sun baras, kuma ba a bari fa a kwashe duka.