PDP ba ta da bakin da za ta soki Buhari – Matawellen Toro
Matawallen Toro kuma Shugaban Jam’iyyar PSP reshen Jihar Filato Alhaji Baban Iya Muhammad ya ce Jam’iyyar PDP ba ta da bakin da za ta tsoma wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, balle ta kai ga sukar tafiyar gwamnatinsa. Alhaji Baban Iya Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda […]
Matawallen Toro kuma Shugaban Jam’iyyar PSP reshen Jihar Filato Alhaji Baban Iya Muhammad ya ce Jam’iyyar PDP ba ta da bakin da za ta tsoma wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, balle ta kai ga sukar tafiyar gwamnatinsa.
Alhaji Baban Iya Muhammad ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce rashin tunani ne Jam’iyyar PDP ta ce za ta soki Buhari kan tafiyar gwamnatinsa.
Ya ce “Jam’iyyar PDP ne ta kashe kasar nan ta cuci talakawa. A lokacin mulkinta babu tsaro babu magani a asibitoci, babu wutar lantarki, babu ruwan sha, komai ya lalace. Ganin haka ya sa talakawan Najeriya suka fito suka zabi Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa, don ya magance matsalolin da PDP ta kawo wa Najeriya. Don haka babu wata magana da PDP za su gaya wa talakawan kasar nan.”
Alhaji Baban Iya ya ce babu yadda za a yi Jam’iyyar PDP ta zama jam’iyyar adawa mai mutunci a Najeriya, domin ana yin adawa ne don taimaka wa talakawa, ita kuma PDP ta kashe talakawan ne.
Ya ce “Idan PDP ta ci gaba da sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari za mu fito mu caccake ta. Domin mu ne muka zabe shi kuma shi ne muke so ya shugabanci kasar nan.”
Baban Iya ya ce Shugaba Buhari yana bin harkokin mulkinsa a natse, yana tsara hanyoyin da zai sake ceto kasar nan daga halin da take ciki ne. Don haka ya yi kira ga talakawan Najeriya su kara jan damara wajen kare Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya samu damar aiwatar da kudirorin da ya sanya a gaba.