PDP ce za ta lashe zaben kananan hukumomin Sakkawato – Sakatare
Aminiya: Ko Jam’iyyar PDP za ta shiga zaben kananan hukumomin da za a gudanar a Jihar Sakkwato ganin an daina jin duriyarku?Kabiru Aliyu: Hakika za mu shiga zaben kananan hukumomin da hukumar zabe ta jiha ta shirya gudanrwa a ranar 12 ga Maris din bana, a yanzu ma mun kammala zabubbukan share-fage a kananan hukumomi […]
Aminiya: Ko Jam’iyyar PDP za ta shiga zaben kananan hukumomin da za a gudanar a Jihar Sakkwato ganin an daina jin duriyarku?
Kabiru Aliyu: Hakika za mu shiga zaben kananan hukumomin da hukumar zabe ta jiha ta shirya gudanrwa a ranar 12 ga Maris din bana, a yanzu ma mun kammala zabubbukan share-fage a kananan hukumomi 23 na jihar, inda muka yi zabe a wasu kananan hukumomi wasu kuwa muka sasanta su kuma aka samu daidaituwa. Ba kamar a Jam’iyyar APC da wasu shugabanninta suka tsayar da yaransu takara jama’ar gari suka ki aminta da hakan, kowannensu ya ja daga, ka ga dole a samu rikici, duk inda aka aza wa mutane wanda ba su so dole ne rigima ta kaure abin ya zama fada. Muna hangen tarwatsewar Jam’iyyar APC ta Sakkwato tunda suka sanya almundahana da yaudara cikin zaben share-fagensu.
Misali mako daya an kasa bayyana wanda ya yi nasara a karamar Hukumar Sakkwto ta Arewa ana ta kiki-kaka, wanda mabiya ke so daban da wanda jagorori ke so, wannan rashin adalcin yana iya zama sanadiyar su rasa nasara a zaben kananan hukumomin. A baya jam’iyyarmu ta PDP ta yi irin wannan kuskure amma yanzu mun gode Allah mun fahimci a tsarin siyasa in kana son nasara dole ka bar mutane su zabi wanda suke so su tsayar. A wuraren da aka ci gaba duk inda aka aza masu wanda ba sa so a jam’iyyarsu sukan yi fatali da shi su zabi wanda ya cancanta a wata jam’iyya da ba ta su ba.
Aminiya: Yaya za ka kwatanta tafiyar gwamnatin Jihar Sakkwato?
Kabiru Aliyu: Gaskiya mun yi nazarin cewa wata takwas a tafiya ta shekara hudu ba zai isa a yanke hukunci kan gwamnati ba. Amma duk da hakan gwamnatin ba ta yi wata hobbasa game da sha’anin tattallin arziki da ciyar da al’umma gaba ba, haka a bangaren yaki da talauci da inganta noma da ilimi domin a halin da ake ciki wadannan abubuwan sun lalace kwarai da gaske gara inda aka fito da yanzu. Amma dai wata takwas bai isa a yanke wa gwamnati mai ci hukunci ba. Sai dai akwai abin lurs a lokacin da APC ke yakin neman zabe ta yi alkawura da dama ko da gangan ko akasin haka, ba ta sani ba cewa ba za ta iya cika su ba. Misali ka ce za ka ba duk wanda bai da aiki a Najeriya Naiar dubu biyar a wata kila za ka ba mutum dubu 75 in babu tsari mai kyau a iya kara 25 saman wadannan da ba su da abin yi, in matasa kawai kake magana kawai za su kai miliyan 35 ko fiye da haka. Duk yadda ka dauko dai har yanzu babu ingantacciyar kididiga ta matasan da ba su da aikin yi a kasar nan ko yawan nakasassu, kuma wurin tantancewa ana iya haduwa da matsaloli na mamaya da zurmuke da samar da amfani ga mutum. Akwai bukatar gwamnati ta dauki tsattsauran mataki kan wannan halin da muke ciki a yanzu na faduwar arzikin man fetur, ban yi tsamnami gwamnati na iya gudanar da wannan aikin ba.
Aminiya: A matsayinka na wanda aka san shi da noma a jihar nan kana ganin kusan Dala miliyan 25 da gwamnatin Sakkwato ta ware don gina masana’antar sarrafa amfanin gona daidai ne?
Kabiru Aliyu: Maganar ai ta yi shiru, mu a nan Sakkwato mun gaji da hattara sa ba mu ga kaho ba, gwamnatin da ta gabata ta ware sama da Naira biliyan hudu da sunan taimakon manoma da noma a Jihar Sakkwato, amma ba mu gani a kasa ba, don haka nake zaton ko wannan ma labari ne kawai. Abin lura kawai dole ne dukanmu ’yan kasa mu sadaukar in har dai canjin da mutane suka nema da gaske suke yi. Ka ga misali a nan Sakkwato akwai hakkin ma’aikata da ya kamata a biya su amma ba su samu ba, albashi mafi karanci na Naira dubu 18, ba kowane ma’aikaci ne ke karba ba. Duk da tsarin ba a kammale ake gabbatar da shi ba kuma gwamnati ba ta yi bayanin taimako ne ko kyautata jin dadin ma’aikata ne ba mu sani ba, amma dai abin da muka tabbatar ma’akata ne daga masu karbar Naiar dubu 15 har kasa ga hakan akwai ga suna birjik. To a yanzu in har an fara fito da maganar ana iya biya ko ba a iya biya matakin albashin to ya kamata a fara yi wa Sakkwatawa bayanin matakin albashin farko kafin daukar wani mataki don ya kamata mu san ma’aikata da wadanda ake tallafawa, ga ariyas na fansho da garatitu, in aka hada su duka ana bin gwamnati Naira biliyan 18. An yi ta alkawarin za a biya amma har yanzu shiru kake ji, duk da Gwamna ya nemi aron kudi a Gwamnatin Tarayya don biyan kudin kuma an ba shi, amma ba labarin zai biya har yanzu. Ya kamata gwamnati ta yi mana bayanin dalilin tsaikon da aka samu. Kuma a matakin gwamnatin Sakkwato kadai ne aka yi musayar mulki ba tare da sanar da jama’a abin da aka gada na bashi ba, masu ruwa da tsaki a jiha sun yi ta kira a gaya wa jama’a lamarin da ke boye tun da hakkinsu ne amma gwamnati ta ki, kila wannan na daga cikin abin da ke damun Gwamnan har ya kasa samun gindin zama a jiharsa.