PDP da APC kar-ta-san-kar ne

Idan zama tsakanin mata da miji ya qi yin daxi, ana ta samun matsaloli iri daban-daban, ‘yan uwa da abokan arzikin miji, waxanda suka isa a idanunsa, masu ba shi shawara ingantacciya ya yi aiki da ita, kan ce da shi  ya qara auren wata mata. An yi amanna cewa yin haka  zai rage yawan […]

PDP da APC kar-ta-san-kar ne

Idan zama tsakanin mata da miji ya qi yin daxi, ana ta samun matsaloli iri daban-daban, ‘yan uwa da abokan arzikin miji, waxanda suka isa a idanunsa, masu ba shi shawara ingantacciya ya yi aiki da ita, kan ce da shi  ya qara auren wata mata. An yi amanna cewa yin haka  zai rage yawan tashin tashinar da ke wakana a gidansa, ya kuma sanya uwargidansa da amaryar da ya auro yin gasa wajen kyautata masa da yi masa ladabi da kuma gaggauta biya masa dukkan buqatunsa.

Irin abin da ake gani  zai iya faruwa ke nan a fagen siyasar qasar nan, talakawa za su yi wa uwargidansu, watau jam’iyyar APC  mai gwamnati  kishiya, domin kuwa da yawa na kukan cewa hankulansu ba su kwanciya da ita, sa’annan kuma tana yawan juya musu baya, ta fita hanyarsu, ba abin da ya dame ta da halin da suke ciki, walau mawuyaci ne ko kuma mai tsananin wahalarwa. Dalili kuwa shi ne tsohuwar uwargidansu, watau jam’iyyar PDP da suka yi wa saki guda, ta  tuba ta kuma yi nadamar abubuwan da ta aikata har hakan ya kai ta ga zamewa bazawara. To, tun da an ce matar na-tuba ba ta rasa miji, idan talakawa suka fahimci ta shiga taitayinta a daidai lokacin da suka yi ilmin-karvi-a-jika suna iya sasantawa da ita, su mayar da ita xakinta.

A yanzu dai jama’a na kukan cewa jam’iyyar APC ta juya wa alqiblarta baya, kuma ba ta da shugabanni na gari da za su iya yi mata jagoranci zuwa  tudun-,mun-tsira. Idan ban da Shugaba Muhammadu Buhari babu wani mutun guda a cikinta da zai yi kira a hnzarta amsa masa, har a garzayo da sauri. Babu wanda zai  bayar da umurni ya ga aiki da cikawa, babu kuma wanda zai  hana a bari har abada. Rikice-rikice sun bi sun dabaibaye jam’iyyar APC har ma ta kasa gudanar da taron qa’ida na shekara bibbiyu don tava-alli wajen kaxa zaren saqar sababbin manufofi da sassaqe wasu shugabannin da ake gani amfaninsu ya daxe da qarewa  da kuma xora jam’iyyar bisa wani sabon tafarkin da zai  qara qarfafata wajen bin manufofi da biyan buqatun ’ya’yanta. 

Manyan cikin jam’iyyar APC sun kasa haxa kawunansu, kowa ta-kansa yake yi don ya ga turbar da ake bi ba za ta fitar da su daga qungurmin dajin da ake ciki ba. Da yawa  kuma sun kama gabansu domin sun fahimci ba da gaske ake yi ba, alqawurran da aka xauka sun sheqe, an kuma mance da talakan da ya yi haqilo cikin rana da ruwa da iska domin kafa gwamnati, ana ta biye son zuciya da  hanqoron neman abin duniya.  Gwamnonin jihohi na jam’iyyar APC sun fita harkar kowa, sun kuma kasa aiwatar da abubuwan da suka  alqawarta, har talakawa suka amince da su. Ba abin da ya dame su face fadar gwamnatinsu da yadda za su kyautata wa maqararrabansu. Babu wanda ya isa ya tuhume su kan  dukiyar talakawan da suke ta tumurmusa, shi kuwa mai ita ko oho. An mayar da shi  tamkar dokin sukuwa, ana ta sukwanarsa ba shi da bakin magana. 

Rigingimu sun dabaibaye  uwar jam’iyyar APC,  manyan jami’an fadar Shugaban Qasa ba su ko-ga-maciji tsakaninsu, kowa na neman kai xanuwansa qasa.  Abin takaici game da haka talaka ne dai abin ke shafa, shi ne kuma aka bari cikin baqar wahala da fatara da mayatar da ba ta misaltuwa. Ta xaya vangaren kuma ana ganin cewa jam’iyyar PDP ta ga haza, kuma a shirye take ta canja kixa domin ’ya’yanta su canja rawar da za ta burge talakawa. Ta  xauki  alwashin kama hanyar inganta tsarin dimokuraxiyyar cikin gida, da kuma sake shiri irin na ragunan da ke karo, suna ja da baya don sake gwabzawa.

Talakawan dai a halin yanzu cewa suke sun dawo daga rakiyar APC a jihohi  da yawa da take mulki,  sun kuma  fara haxa kai da ’ya’yan jam’iyyar PDP da suka yi likimo bayan shan kaye a zaven 2015, suna tsara yadda za su tunkari al’amuran siyasa nan gaba. Kamar yadda suke nunawa, za su tsaya su kalli kamun ludayin jami’iyyun  PDP da ta APC a tsanake, sa’annan su ga wacce za su tafi tare da ita idan zaven 2019 ya zo. Jam’iiyar PDP dai a nan yankin Arewaci ba kanwar lasa ce ba, tana da gogaggun shugabannin da suka jajirce wajen xaukaka matsayinta, sun kuma  samu nasarori masu yawan gaske tun daga 1999, lokacin da aka mayar da mulki hannun farar hula. Ta  kame jihohi sama da sahirin  kafin guguwar Buhari ta zo ta fara xaixaita su a shekarar 2003. Nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a kwanan nan  a zaven cike gurbi na xan majalisar dattijai a Jihar Osun, inda APC ta yi kaka-gida abu ne da ya qarfafa zukatan xaukacin ’yan jam’iyyar PDP a qasar baki xaya, sun kuma quduri aniyar sake maimata haka a zavuvvukan qananan hukumomi a jihohin da ke janjani, har yanzu ba su yi nasu ba.

Har yanzu dai ana ganin cewa shugabannin  jam’iyyar APC sun kasa gwada wa  mabiyansu ingantaccen shugabancin da zai kai ga xaga martaba da kuma kare ta daga dukkan fitintinun da ke wahalar da ita. Kuma sun kasa qago wasu dabarun hana ’ya’yanta zaizayewa, ko  magance harigodon da ke faruwa a jihohi tsakanin gwamnoninta da kuma gagga-gaggan ‘ya’yanta.  A maimakon haka sai shugabannin suka duqufa kan farfagandar da ba ta da wani amfani ga talaka sai dai ga gwamnonin da ake kwana, ana wuni wajen kwarzantawa, alhali kuwa babu wani abin-ku-zo-ku-gani da suke tsinanawa.

Ana ganin cewa jam’iyyar  APC ma ta kauce hanya daidai da yadda ta PDP ta yi a baya, kuma bisa ga dukkan alamu wacce ke adawa ce  ke  qoqarin murmurewa, domin kuwa ita ce ke da abubuwa da yawa da za ta gorantawa ta APC, wacce  take ganin cewa ta jefa kanta cikin mawuyacin halin da zai yi wuya ta fitar da kanta. Ita kuwa jam’iyyar APC a yanzu ne take neman janyo ‘ya’yanta  a jika domin su bayar da gudummawa ga gwagwarmayar da jam’iyyar ta saba yi  tun farkon kafuwarta,  har kuma  ta kai ga danqar ragamar mulki. Maganar  yi mata kishiya bai taso ba a gare ta, domin ai an tava zama tare, kuma kar-ta-san kar. To  wai shin kishiya tana da rana  kuwa?  Bayyanar jam’iyyar PDP da qarfinta a fagen siyasar Najeriya zai yi wani tasiri kuwa? E, hakan zai iya  sanya  shugabannin jam’iyyar APC su canja salo don a kai ga canjin da suke tinqaho da shi, idan kuma suka shantake sai kawai su ma a  canja su cikin ruwan sanyi.  

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos