PDP da zargin musuluntar da Najeriya

A ranar 7 ga Janairun da ya gabata ne jaridun kasr nan suka ruwaito wata kungiya mai suna Majalisar karfafa Daidaito a Tsakanin Addinai (Religious Ekuity Promotion Council – REPC) tana zargin babbar jam’iyyar adawa ta kasar nan wato Jam’iyyar APC da cewa an kafa ta ne domin biyan bukatun Musulmin kasar nan. Kuma ta […]

PDP da zargin musuluntar da Najeriya
PDP da zargin musuluntar da Najeriya

A ranar 7 ga Janairun da ya gabata ne jaridun kasr nan suka ruwaito wata kungiya mai suna Majalisar karfafa Daidaito a Tsakanin Addinai (Religious Ekuity Promotion Council – REPC) tana zargin babbar jam’iyyar adawa ta kasar nan wato Jam’iyyar APC da cewa an kafa ta ne domin biyan bukatun Musulmin kasar nan. Kuma ta alakanta APC da kungiyar Ikhwanul Muslmina ta kasar Masar.
kungiyar wadda ba sananniya ba ce ta fadi a wata sanarwa da Babban Sakataren Rabaran Tanko Garba ya sanya wa hannu cewa tana da ja kan shugabbanin kwamitin rikon Jam’iyyar APC na kasa inda ta yi zargin an tauye Kiristocin da ke cikin jam’iyyar. Ta ce galibin shugabannin kwamitin da masu sha’awar tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin APC Musulmi ne da suke da niyyar musuluntar da Najeriya kamar kungiyar Ikhwanul Muslimina ta kasar Masar.
kungyar REPC ta jero sunayen wasu wakilan kwamitin rikon Musulmi da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar Musulmi domin kafa hujja kan zarginta.
Sai dai Sakataren Watsa Labarai na kwamitin rikon APC na kasa Lai Mohammed ya yi fatali da wannan zargi, inda ya ce kwamitin rikon yana da wakilai 35, kuma Musulmi 18 ne kawai a cikinsu. “Akwai wakilan kwamitin riko 35: Kiristoci 17, Musulmi 18. Shin wannan zubi ya yi kama da Jam’iyyar Musulunci?” Lai ya tambaya.
Lai Mohammed ya ce kada masu zargin su mance Jam’iyyar APC tana da wakilai a majalisa da gwamnoni da suka fito daga sassan kasar nan. Don haka sun damu kan yadda wasu da ba su da wani abu da za su gabatar domin ci gaban kasar nan su nemi mayar da kasar nan baya ta hanya shara irin wannan karya.
Y ace babu wata jam’iyyar siyasa a kasar nan da za a kafa ta kan kabilanci ko addini, kuma jam’iyyarsu za ta rungumi dukkan addinai, sannan abin da jama’a suke bukata shi ne me kowace jam’iyya za ta iya gbatar musu.
Washegarin wannan korafi na kungiyar REPC, sai ga Jam’iyyar PDP ta hannun kakakinta na kasa Olisa Metuh  tana cewa wai yunkurin Jam’iyyar APC na musulntar da Najeriya ne ya sa ’ya’yan jam’iyyar suka tashi tsaye wajen neman mulki ido rufe. Kuma wani abin mamaki PDP ta kasa gane cewa wanda ya yi wannan zargi Rabaran ne, inda ta dauka wata kungiyar Musulmi ce ta yi wannan korafi, wannan ya sa Metuh ya ce: “Muna godiya ga daukacin ’yan Najeriya musamman Musulmin kwarai kan fallaswa da kin shiga APC da mugun shirinta. Yanzu da aka fallasa wannan shiri nasu, muna shawartar shugabannin APC su sauya salon tafiyarsu su daina mugun shirinsu.”
Wannan ne ya sa kakakin APC Lai Mohammed ya sake mayar da martani inda ya ce PDP ta haukace inda take kokarin bata sunan jam’iyyar adawar. Ya ce kafin hadewar jam’iyyun da suka kafa APC ana kallon jam’iyyun a matsayin na yankuna. Kuma sakamakon karfin da tagomashin da APC ke samu, sai PDP ta koma ga yi mata kazafin zama jam’iyyar addini.
Ya ce PDP tana kokarin yin haka ne domin kawar da hankalin ’yan Najeriya daga ainihin gazawarta wajen magance matsalolin kasa. Ya ce: “Ba addini ne matsalar ’yan Najeriya ba, matsalolin da suke addabarsu su ne rashin aikin yi da cin hanci da rashawa da almundahana da bacewar biliyoyin Dala daga Kamfanin Mai na kasa da kuma kudaden da aka yi amfani da su aka sayo motoci masu sulke ga Ministar Sufurin Jiragen Sama.”
Ban so cewa komai kan wannan sabon zargi ba, amma ganin yadda Jam’iyyar PDP ke kokarin fakewa da addini domin boye gazawarta a fagen mulki bayan shekara 15 tana shugabancin kasar nan ya zame dole mutane irina mu ce wani abu.
A ganina wannan kungiya da ta yi wancan zargi ga APC, babu ita, Jam’iyyar PDP ce kawai ta kirkiro sunan domin ta samu hanyar da za ta alakanta APC din da Musulunci domin bata mata suna. PDP ta kware wajen kirkiro kungoyoyin domin yin amfani da su ta zame kafofin abokan adawa. Na san ba mu manta da jabun APC da ta nemi rajista da INEC ba, domin hana APC samun rajista da wannan suna, inda a karshe aka gano daga shafin intanet na PDP ake shirya komai. Ina so a fahimci cewa ni da dan APC ba ne, amma batun makomar kasar nan hakki ne da ke kan kowanennmu, bai kamata mu bari saboda son ran wasu kalilan a jefa kasarmu a cikin bala’i ba.
Ba wannan ne karo na farko da PDP ke amfani da addini ba wajen boye gazawarta da kuma neman tagomashi daga jama’a. Lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya fito takara a karon farko a shekarar 2003, PDP ta yi amfani da addini wajen bata shi, inda ta ce ya ce wai kada a zabi wanda ba Musulmi ba, duk da cewa abin da Buhari ya ce shi ne mutane su tabbatar sun zabi mutum nagari wanda zai kare musu mutunci da addini da rayuwa da dukiya. Amma sai PDP ta rika amfani da ’yan kanzaginta a kafafen watsa labarai suna cewa Buhari mai tsananin ra’ayin addini ne da in ya ci zabe zai musuluntar da Najeriya!  Da wannan aka sanya tsoro a zukatan wadanda ba Musulmi ba game da takarar Buhari, har aka samu aka yi zaben da duniya ta tabbatar cike yake da mugun magudi da rashin tsabta! Amma tunda Buhari aka tauye a tunanin jama’a shi ke nan aka zauna lafiya!
Haka da aka zo zaben shekarar 2007, aka tukuikuya aka tafka magudi domin dai PDP ta ci gaba da mulki koda kasar za ta rushe ta lalace, aka tsara sakamakon zabe a wani otel a Abuja kafin a gudanar da zaben aka ba dan takarar PDP kuri’un da ko hankali ba zai yarda da shi ba, sannan aka ba Buhari kuri’un da aka ga dama.
Da zaben shekarar 2011 ya zo, nan ne PDP ta fi amfani da addini a siyasar Najeriya, inda bayanai suka nuna coci-coci da dama sun haramta wa wakilansu zuwa coci ba tare da katin rajista ba, kuma suka umarci wakilansu su tabbatar dan takarar PDP suka zaba saboda shi ne dan addininsu. Shugaban da ya yi alkawarin zai hada mu da sabuwar iskar shaka mai dadi, amma aka wayi gari ya hada mu da muguwar iskar shaka mafi muni da ta kada a Najeriya.
Gazawar gwamnatin PDP a karkashin Jonathan ba abu ne da ke bukatar bayani ba, babu wani bangare da za ka dauka ka nuna ta yi abin kirki a kai. Kai saboda yadda al’amura suka tabarbare ne ya sa tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Jonathan wasika mai shafi 18 yana nuna masa halin da kasa ke ciki domi ya dauki mataki. Amma sai Shugaba Jonathan ya sanya wasikar a kwandon shara, wanda haka ne ya sa Cif Obasanjo ya fusata ya mika wa manema labarai wasikar domin duniya ta ji.
Na yi imani da Obasanjo Musulmi ne da PDP ta fito ta jingna shi da Boko Haram ko Ikhwanul Muslimina ko wata kungiya mai tsaurin ra’ayin addini. Kuma maimakon Fadar Shugaban kasa ta duba wasika da idon rahama ta yi gyara a inda ya kamata domin amfanin kasar nan, sai ta koma tana zargin cewa ai shi ma Obasanjo lokacin mulkinsa ya yi irin wannan.
Gazawar Shugaba Jonathan ta mayar da shi wani shugaba da ya zama mai kamun kafa a coci-coci inda galibin kalamansa kan al’amuran kasa dga coci yake furta su, ya manta shi Shugaban Najeriya ne na Musulmi da Kirista da marasa addini.   

Abdulkarim dayyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,
08023106666, 08060116666
Imel:[email protected]

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno