PDP da zargin musuluntar da Najeriya (2)
Gazawar Shugaba Jonathan ta mayar da shi wani shugaba da ya zama mai kamun kafa a coci-coci, inda galibin kalamansa kan al’amuran kasa daga coci yake furta su, ya manta shi Shugaban Najeriya ne na Musulmi da Kirista da marasa addini. Ba mu ce kada Shugaba Jonathan ya je coci ba, amma ya je domin […]
Gazawar Shugaba Jonathan ta mayar da shi wani shugaba da ya zama mai kamun kafa a coci-coci, inda galibin kalamansa kan al’amuran kasa daga coci yake furta su, ya manta shi Shugaban Najeriya ne na Musulmi da Kirista da marasa addini.
Ba mu ce kada Shugaba Jonathan ya je coci ba, amma ya je domin ya yi ibada ba domin ya yi kamfe ba, balle ya saki baki kan abubuwan da suke da muhimmanci a al’amuran kasa. Misali daga cikin kalaman da ya furta a coci akwai cewa akwai ’yan Boko Haram a gwamnatinsa, akwai su a cikin sojoji, akwai su a cikin ’yan majalisar dokoki, kai wasu ma suna cin abinci tare da shi! Wadannan mutane ne fa a yanzu kusan kullum suke kashe daruruwan mutane a Arewa maso Gabas, Shugaban kasa yana ji yana gani, ba tare da ya dauki matakin fallasa wadannan ’yan Boko Haram da suke cikin gwamnatinsa ba.
Ina wakilan Majalisar Dattawa? Ina wakilan Majalisar Wakilai? Me kuke jira ba za ku gayyaci Shugaba Jonathan ya fallasa sunayen ’yan Boko Haram da suke cin abinci tare da shi ba, domin a tuhume su in an same su da laifi a hukunta su?
Mu koma kan batun zargin musuluntar da Najeriya da PDP ta zargi APC da shi, tambayar da za mu yi ita ce shin PDP ta kiristan da Najeriya ne, shi ya sa take tsoron kada APC ta musuluntar da kasar? Ko kuwa yawan Musulmi a cikin shugabannin Jam’iyyar APC shi ne alama ta za ta musuluntar da kasar nan?
Kamar yadda na fada a baya ni ba dan Jam’iyyar APC ba ne, kai cikin manyan jam’iyyun kasar nan tun dawowar mulkin farar hula a 1999 ban taba shiga cikin daya daga cikinsu ba. Ban taba yin APP ko ANPP ko CPC ba, duk da cewa ni masoyin Janar Buhari ne. Haka ita ma PDP ban taba shiga cikinta ba, saboda dukkansu ban gamsu da manufofinsu ba, ko kuma ban dauka za su iya magance matsalolin kasar nan ba. To amma a matsayina na dan kasa mai kishinta da bukatun kasar suke gaba da bukatuna, ba zai yiwu in yi shiru ba a lokacin da na ga PDP tana shirin jefa kasar nan a cikin bala’in da ba a san inda zai tsaya ba.
Hakika ga alama PDP ta kiristansar da kasar nan ne ya sa take kokarin zargin APC za ta musuluntar da ita in ta cin zabe. Na fadi haka ne saboda lokacin da na ga wannan zargi sai na ce bari mu duba jerin shugabbanin kasar nan a karkashin PDP mu ga su wane ne suka fi yawa a cikinta.
Majalisar Dokoki:
Bayan zaben shekarar 2011, PDP ta tsara wani shiri wanda ga alama da niyya aka shirya shi domin an jingine Musulmin da suka fito daga kabilun Hausawa da Fulani da Bare-bare da Nufawa, musamman a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai. Misali da aka tashi zaben Shugaban Majalisar Dattawa PDP ta kebe shi musamman ga Sanata Dabid Mark, Kirista dan kabilar Idoma daga Jihar Benuwai, sai Sanata Ike Ekweremmadu, Kirista dan kabilar Ibo daga Imo, sannan Shugaban Masu Rinjaye aka ba Sanata bictor Ndoma Egba, shi ma Kirista daga Kudu maso Kudu. Wadannan su ne manyan shugabannin Majalisar Dattawa babu Musulmi a cikinsu. Sannan da PDP ta tashi tsara yadda shugabannin Majalisar Wakilai za su kasance, sai ta ce Mulikat Akande Bayarbiya Musulma daga Kudu maso Yamma ta zama shugaba, sannan Yakubu Dogara, Basayi Kirista daga Jihar Bauchi ya zama mataimakinta. A nan ma an jingine manyan kabilun Arewa hudu da Musulmi suka fi rinjaye da muka ambata a baya.
Tsaro:
A bangaren tsaro tun hawan Obasanjo PDP ta fara nuna alamun za ta jingine Musulmi da suke fito daga wadannan manyan kabilu hudu, idan za a nada wani jigon tsaro daga Arewa sai a dauko Kirista daga karamar kabila ya zama wakilin Arewa, saboda a tunzura Musulmi wadanda su ne mafiya rinjaye su yi magana a samu rarrabuwar kawunan ’yan Arewa. An san muna da kananan kabilu da dama da galibinsu Kiristoci ne, su kuma a can Kudu maso Yamma wadanda kabilarsu dayan ne, wato Yarbawa sai Obasanjo ya dakile Musulmin yankin daga samun koda mukaman ministoci ne har sai da suka gaji suka yi magana, to amma tunda kabila daya suka fito sai matsalarsu ta zamo da sauki, Obasanjo ya dauko Musulmin ya tsarma a gwamnatinsa. Tunda muna da manyan hafsoshin tsaro guda hudu ne Babban hafsan Tsaro (CDS) da Hafsan Hafsoshin Sojan kasa da Hafsan Hafsoshin Sojan Sama da Hafsan Hafsoshin Sojan Ruwa akalla a ba Musulmi Bahaushe ko Bafullatani ko Babarbare ko Banufe daya ko biyu daga cikin wadannan mukaman, amma sai aka rika yin akasin haka, Musulmin da suka fito daga wadannan kabilu hudu suka danne zuciyarsu aka tafi a haka.
Da Jonathan ya hau mulki bayan rasuwar marigayi Shugaba ’Yar’aduwa yana kakkabe manyan hafsoshin da ya gada, a daddafe ya nada Musulmi daya a mukamin Hafsan Sojan Sama. Daga baya ya cire shi, kuma bai mayar da Musulmi a madadinsa ba, da ya tashi dauko magajinsa sai ya dauko Kirista daga Adamawa ya nada, wanda yanzu shi ne Babban Hafsan Tsaro. A bara bayan tashim bam a barikin soja na Jaji jaridar Daily Trust ta ce ritayar da aka yi wa wasu hafsoshin soja da suka fito daga Arewa wadanda galibinsu Musulmi ne da suka fito daga wadancan manyan kabilu hudu, an yi ne domin share fage ga Manjo Janar Minimah dan kabilar Shugaba Jonathan don ya karbi ragama daga Janar Ihejirika. Kwatsam sai hakan ya tabbata a bana.
To amma babban abin takaicin shi ne cikin wadannan manyan kabilu hudu na Arewa ba daya daga aka dauka aka nada kan daya daga cikin wadannan muhimman mukamai guda hudu. Sai aka fifita kabilanci a kan addini domin a dada gwara kan al’ummar Arewa a sanya gaba da kiyayya a tsakanin Musulmi da Kiristan yankin. Dalili idan Musulmin da suka fito daga wadancan kabilu hudu da muka ambata suka yi magana, sai a ce ba sa son sauran kabilun yankinsu.
Manyan hafsoshi hudun ynzu su ne Janar Kenneth Tobiah Jacob Minimah Babban Hafsan Sojan kasa Kirista dan kabilar Ijaw kabilar Shugaba Jonathan daga kasar Opobo ta Jihar Ribas.
Sai Riyal Admiral Usman OYIBE Jibrin, Musulmi dan kabilar Ibira daga Jihar Kogi Babban Hafsan Sojan Ruwa.
Iya Marshal Adesola Amosun Bayarbe daga Jihar Legas ban san addininsa ba, Babban Hafsan Sojan Sama, yayin da Iya Marshal Aled Badeh, Kirista daga Jihar Adamawa Babban Hafsan Tsaro. Musulmi Bahaushe ko Bafullani ko Babarbare ko Banufe ba su da ko daya duk da cewa su ne manyan kabilun Arewa!
Sannan kwamandojin manyan rundunonin sojan kasar nan biyar (GOCs) daya ne kawai Musulmi da ya fito daga cikin wadannan manyan kabilu hudu. Ga jerinsu nan Manjo Janar Kingsley Osuji, Babban Kwamandan Runduna ta daya da ke Kaduna; Manjo Janar EF Abejirin, Babban Kwamandan Runduna ta Biyu da ke Ibadan; Manjo Janar JS Zaruwa, Babban kwamandan Runduna ta Uku da ke Jos; Manjo Janar TI Dibi, Babbann Kwamnadan Runduna ta 81 da ke Legas sai Manjo Janar AT Yusuf, Babban Kwamnadan Runduna ta 82 da ke Enugu. Ashe babu mamaki idan PDP ta zargi APC da cewa tana yunkurin musuluntar da Najeriya.
Yanzu kuma lamarin ya dawo kan Gwamnan Babban Banki Sanusi Lamido Sanusi, shi ma an kore shi da wayo za a nada mutumin yankin Shugaban kasa kuma Kirista a kuejrarsa, kun ga an dada kiristantar da Najeriya ta yadda za a ji dadin kamfen din yakar APC ko duk wani yunkuri na kawar da gwamnatin PDP da ta gaza a shekara 15 na mulkin da take yi a kasar nan ta amfani da addini da kabilanci! Ya kamata ’yan Najeriya su farka su ki amincewa da wannan salon a fakewa da addini ko kabilanci ana dora shugabannin da za su kashe kasar nan, in kuma mun ki to za mu ci gaba da ganin abubuwa marasa kyau.
Abdulkarim dayyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,
08023106666, 08060116666
Imel:[email protected]