PDP ga APC: Kada ku mayar da mu bayi
Shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa sun gargadi Jam’iyyar APC cewa kada ta kuskura ta yi yunkurin mayar da su bayi, inda suka zargi APC da kokarin kwace wadansu jihohi da PDP ta ci a zaben gwamnonin da ya gabata. Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata a Abuja, Sakataren Watsa labarai na Jam’iyyar […]

Shugabannin Jam’iyyar PDP na kasa sun gargadi Jam’iyyar APC cewa kada ta kuskura ta yi yunkurin mayar da su bayi, inda suka zargi APC da kokarin kwace wadansu jihohi da PDP ta ci a zaben gwamnonin da ya gabata.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata a Abuja, Sakataren Watsa labarai na Jam’iyyar PDP ta kasa Mista Olisa Metuh, ya yi zargin cewa Jam’iyyar APC na kokarin tunzura jama’a a jihohin Ribas da Akwa Ibom da sauransu inda PDP ta samu nasara, alhali ita PDP ta kawar da kai ne daga wasdanu zarge-zarge na magudin zabe da aka gudanar a wadansu jihohin Arewa.
Mista Olisa Metuh ya ce: “A wadansu jihohin Arewa an ce ba a samu kuri’un da suka lalace ba, misali a Kano, babu ko da kuri’a daya da aka lalata a daukacin jihar. Ke nan suna da wayo kuma suna da digirin digirgir ta yadda suka san yadda za su gudanar da abin ba tare da sun yi wani kuskure ba.”
Sakataren Labaran ya kara da cewa: “Wannan kasarmu ce, amma ba za mu jira a mamaye mu ba. Eh, an shaida mana cewa galibin ’yan Najeriya sun zabi wata jam’iyya. A matsayinmu na ’yan dimokuradiyya, mun karbi hakan. Amma ko a dokokinmu, duk da muna bakin cikin abin da ya faru, ba za mu so a dauke mu tamkar wawaye ba. Kuma bai kamata su dauke mu tamkar bayi ribatattun yaki ba.”
Mista Metuh ya kara da cewa: “Harshen da suke magana da shi a kanmu da yadda suke yin abubuwa suna nuna kamar sojoji ne da suka ci mu da yaki ba mutanen da suke shirye su bi ka’idojin dimokuradiyya ba, maimakon haka sun zo ne domin su dandana wa mutanen da suka ci da yaki da jam’iyyar da suka ci da yaki.”
Ya ce, “Mun tabbatar da dimokuradiyya a shekara 16. Ba su taba karbar mulki ta dimokuradiyya ba, suna fadin karairayi tare da kokarin fusata mutane su jefa dimokuradiyyarmu a cikin matsala. Don haka za mu ci gaba da kare dimokuradiyya. Kuma muna yi musu fatan nasara a shekara hudu masu zuwa wajen kare dimokuradiyya. Amma yadda suke gudanar da abubuwa sun fara taku da kafar hagun.”
Shi kansa shugaba Jonathan a karshen mako a yayin wata addu’ar ban kwana da aka shirya masa a Abuja, ya shawarci ministocinsa su zauna cikin shiri domin akwai yiwuwar za a musguna musu tare da shi kansa.
A jawabin da ya karanta mai taken “Mugun shirin APC game da zabin al’umma a jihohin Akwa Ibom da Ribas da Delta, Metuh ya ce: “A karshe zaben 2015, jagoran jam’iyyarmu Shugaba Goodluck Jonathan a wani yanayi na nuna dattaku ya amince da shan kaye a hannun dan takarar APC Janar Muhammadu Buhari.
Ya ce, “Wannan aiki guda daya ne ya kwantar da kura a kasar nan, ya daidaita al’amuran siyasa kuma ya daukaka martabar dimokuradiyyar kasar nan a idon duniya. Kuma ’yan takararmu na gwamnoni da na majalisu da suka fadi a zabe sun amince da shan kaye domin kare bukatun kasa da tsare dimokuradiyyarmu da hadin kan kasa a matsayinmu na al’umma. Wannan sadaukarwa daga ’yan takararmu ta zo ne duk da magudi da gazawa iri-iri da aka samu a lokacin babban zaben don kayar da jam’iyyarmu. PDP ta karbi sakamakon zaben da zuciya daya ba wai don hanyar da aka gudanar da zaben ba ta da kura-kurai ba ne, sai domin fifita bukatun kasa.”
Mista Metuh ya ce, “Don haka abin damuwa ne duk da samun nasara, APC ta ci gaba da nuna zakewa a kokarinta na kwace daukacin iko da harkokin mulki ta hanyar yunkurin kwace jihohin da a zahiri PDP ce ta lashe zabensu. Idan za ku iya tunawa mun t ba sanar da ’yan Najeriya shirin da APC ke yin a mayar da kasar nan mai bin tsarin jam’iyya daya ta hanyar wargaza PDP, da kwace jihohinmu da kujerun ’yan majalisarmu, duk domin tabbatar da ba a samu kakkarfar adawa ba lokacin da suka hau gadon mulki.”
Ingiza rikici:
Kakakin Jam’iyyar PDP ya kara da cewa: “A yanzu da nake magana, APC ta koma ga ingiza rikici da tunzura jama’a tare da tattaro albarkatu domin ta tilasta bangaren shari’a ya tauye zabin jama’a a wadancan jihohi. Musamman bincikenmu ya gano a jihohin Delta da Akwa Ibom da Ribas, jami’an APC suna aiki gadan-gadan don tabbatar da an juya nasarar PDP da zabenta da jama’a suka yi bisa radin kansu a wadannan jihohi.”
Mista Metuh ya ci gaba da cewa: “Muna sane da babban yunkurin da APC ta yi na saye da sauya ra’ayin wadansu masu ruwa da tsaki a harkokin zabe ciki har da jami’an INEC da na tsaro domin su bayar da shaidu na karya tare da sauya alkaluman zabe don kayar da PDP a kotun shari’ar zabe. Wannan baya ga daukar nauyin tallace-tallacen batanci a wadansu kafafen watsa labarai ne da za a rika shara karya da canja alkaluman zabe don su dace da mugun shirinsu na sauya tunanin jama’a domin hana jam’iyyarmu samun adalci a wadannan jihohi.”
Ya kara da cewa: “Mun san manufar da ta sa APC ta kagu ta kwace wadancan jihohi uku, ita ce yakinin da suke da ita cewa suna da muhimmanci ga PDP, kuma kwace su zai dada raunanawa da karya jam’iyyarmu kuma hakan zai ba da damar mayar da kasar nan mai bin tsarin jam’iyya daya.”
Ba za mu amince da kowane mugun nufi ba
Kakakin na PDP ya ci gaba da cewa: “PDP tana fadi da babbar murya cewa ba za mu amince da duk wani yunkuri daga kowane mutum ba, musamman Jam’iyyar APC ta yi danniya ko ta murde mana nasarar da muka samu a wadancan jihohi ko kwace jiha da wannan batu ya shafa ba. Ta kowace hanya kada APC ta dauki bin doka da ke da asali daga kishin kasarmu a kokarinmu na tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa da kwanciyar hankali a matsayin gazawa. Muna tabbatar wa duniya mambobinmu suna da iko da dama kuma a shirye muke mu kare zabenmu a wadannan jihohi ta bin duk hanyoyin da doka ta tanada.”
Mista Metuh ya kara da cewa: “A matsayinmu na jam’iyyar da ta kafa tarihi wajen rainon dimokuradiyya na tsawon shekara 16 tare da daukaka darajarta zuwa mataki mai inganci da kasashen da suke bin dimokuradiyya a duniya suke yabawa, ba za mu kame hannuwanmu mu zuba ido APC da wakilanta su rusa wannan nasara da aka samu ba. Don haka PDP tana jawo hankalin bangaren shari’a da hukumomin INEC da na tsaro game da mugun shirin da da APC ke yin a tsoma hukumomin nasu da jami’ansu a cikin wannan mugun shiri.”
Sakataren Labaran ya ce: “Bisa lura da abubuwan da muka ambata a sama, muna kira ga wadannan hukumomi su sanya ido sosai a kan jami’ansu da suka taka rawa wajen gudanar da zabe kuma su yi duk abin da ya kamata kamar yadda doka ta tanada wajen kare martaba da mutuncinsu ta hanyar hana masu son kai da miyagun mutane cimma burinsu.”
Sai ya karkare da cewa: “A karshe, yayin da za mu kama Jam’iyyar APC da laifi idan aka samu barkewar rikici a jihohin Ribas da Delta da Akwa Ibom, muna kira ga jama’a su tashi tsaye su kare zabensu ta hanyar bin duk hanyoyin da doka ta tanada domin tabbatar da cewa masu son kai da makiya dimokuradiyya ba su wancakalar da zabinsu da suka nuna ta hanyar kada kuri’a ba.”