PDP ga Buhari: Ka dukufa wajen yin aiki

A jiya Alhamis ne jam’iyyar adawa ta PDP ta gudanar da taron farfado da martabarta domin sake wa jam’iyyar fasali, abin da wasu ’yan jam’iyyar ke ganin zai taimaka wajen dawo da kimar ta ga idon ’yan Najeriya.Har ila yau, ana ganin taron zai taimaka wajen kawo karshen rarrabuwar kawunan da jam’iyyar ke fuskanta da […]

PDP ga Buhari: Ka dukufa wajen yin aiki
PDP ga Buhari: Ka dukufa wajen yin aiki

A jiya Alhamis ne jam’iyyar adawa ta PDP ta gudanar da taron farfado da martabarta domin sake wa jam’iyyar fasali, abin da wasu ’yan jam’iyyar ke ganin zai taimaka wajen dawo da kimar ta ga idon ’yan Najeriya.
Har ila yau, ana ganin taron zai taimaka wajen kawo karshen rarrabuwar kawunan da jam’iyyar ke fuskanta da kuma fatan dinke barakar da ake ganin ta kunno kai a jam’iyyar.
A lokacin taron wanda aka gudanar a Abuja, tsohon Shugaban Jam’iyyar  Dokta Bello Halliru Mohammed ya ce lokaci ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari zai daina ba ’yan Najeriya uzuri ya dukufa da aikin ci gaban kasar nan.
Cikin wadanda suka halarci taron har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu da Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido da tsohon Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Ibrahim Mantu da sauransu.
Kodayake, gabanin taron Shugaban Kwamitin Shiryasa, Raymond Dokpesi, ya nemi gafarar al’ummar kasar nan kan abin da ya kira kura-kuran da jam’iyyar PDP ta tafka a shekaru 16 da suka gabata, da kin aiwatar da tsarin karba-karba da rashin dimokiradiyyar cikin gida da kuma tilastawa ’yan Najeriya tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Sai dai a shekaranjiya Laraba, Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar PDP, Cif Oliseh Metuh, ya mayar da martani ga Mista Dokpesin, inda ya ce gafarar da ya ce jam’iyyar tana nema daga ’yan Najeriya ra’ayin kashin kansa ne ba na  jam’iyyar ba.