PDP ga ’yan Najeriya: Ku gafarce mu
Jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi afuwar ’yan Najeriya game da wasu kurakurai da ta tafka a lokacin da ta mulkin kasar nan tsakanin shekarar 1999 zuwa 2015, inda ta bukaci ’yan kasar nan su gafarce ta, musamman saboda nuna gazawarta wajen biyan bukatun al’umma a tsawon shekara 16 da ta yi a kan mulki.Sakon […]
Jam’iyyar adawa ta PDP ta nemi afuwar ’yan Najeriya game da wasu kurakurai da ta tafka a lokacin da ta mulkin kasar nan tsakanin shekarar 1999 zuwa 2015, inda ta bukaci ’yan kasar nan su gafarce ta, musamman saboda nuna gazawarta wajen biyan bukatun al’umma a tsawon shekara 16 da ta yi a kan mulki.
Sakon neman afuwar jam’iyyar ya fito ne daga bakin shugaban Kwamitin tsare-tsaren babban taron kasa na PDP, wato Raymond Dokpesi, a lokacin da ya gabatar da jawabi ga manema labarai ranar Talata.
“Muna sane da kura-kuran da muka tafka shekaru 16 da suka wuce, a matsayinmu na ‘’yan Adam, dole ne mu yi kuskure, don ba lallai ba ne mu biya dukkan bukatun ‘’yan Najeriya, saboda haka muna neman afuwa,” inji Mista Dokpesi.
“Kada a yi kuskure, Jam’iyyar PDP na sane da cewa an tafka kura-kurai a cikin tafiyar da aka yi.
“Mun amince da cewa a wani lokaci da ya gabata, an yi kura-kurai, ba mu cika burin ’yan Najeriya ba,” inji shi.
Mista Dokjpesi, wand aya yi bayani kan babban taron kasa na jam’iyyar da za a gudanar a Thisday Dome da ke Abuja, ya ce PDP ta koyi darasi daga kura-kuranta, don haka an shirya taron ne don warware matsaloli, ta hanyar nazarin muhimman al’amuran da za samar da dorewar shugabanci nagari da manufofin dimokuradiyya a Najeriya.
Mista Dokpesi ya bayyana kura-kuran da ka tafka da suka hada da kauce wa manufofin wadanda suka kafa jam’iyyar. Kuma yanke mayar watsi da tsarin karba-karba shi ya haifar da halin kak2a-ni-ka yi ga jam’iyyar.
“Kuskuren farko da aka tafka shi ne a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2011, inda aka ki kyale Arewa ta kammala wa’adin mulkinta,” a cewarsa.
Mista Dokpesi ya bayyana cewa, babban taron kasar zai nuna wa ’yan Najeriya cewa, shugabgannin PDP a shirye suke wajen kawo gyara.
A cewarsa, al’amuran da suka faru a zaben da ya gabata, sun sanya dole a tattaro daukacin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP, don tattaunawa kan halin tda jam’iyyar ke ciki, su kuma bayar da shawarar da za ta kai ga jam’iyyar ta sake samun ragamar mulki a kowane mataki a daukacin fadin kasar nan.
Ya ce jam’iyyar PDP na shirin mayar da akalar jam’iyyar ta zama ta matasa.
Dangane da manufar jam’iyyar, ya ce fiye da kashi 50 cikin 100 na mahalarta taron da aka gudanar jiya Alhamis matasa ne da aka zabo su daga kananan hukumomi 774 da ke daukacin fadin Najeriya.
“Mun yanke matsayar zakulo matasa daga kananan hukumomi 774, wadanda shekarunsu ke kasa da 35, kuma suke da digiri ko kwatankwacinsa, a matsayin wkailan da za su halarci wannan babban taro,” inji shi.
Sai dai kuma Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa Oliseh Metu, ya ce wannan ra’ayin Dokpesi kawai, domin ita jam’iyyar PDP ba ta yi nadamar tsayar da Jonathan takara ba, saboda haka ba za ta nemi gafarar kowa ba saboda abin da ta aikata.