PDP na bukatar shugaba nagari – Gbenga Daniel

Tsohon Gwamnan Jahar Ogun, Gbenga Daniel kuma wadda ya nuna sha’awarsa ta tsayawa neman shugabancin jam’iyyar PDP a Najeriya, ya hori wakilai (Delegate) na jahar jigawa da su tsaya su yi zaben shugaban jam’iyya nagari domin samun shugaban kasa nagari wadda zai yi adalci ga kowa a fadin Najeriya. Tsohon gwamnan ya fadi haka ne […]

PDP na bukatar shugaba nagari – Gbenga Daniel

Tsohon Gwamnan Jahar Ogun, Gbenga Daniel kuma wadda ya nuna sha’awarsa ta tsayawa neman shugabancin jam’iyyar PDP a Najeriya, ya hori wakilai (Delegate) na jahar jigawa da su tsaya su yi zaben shugaban jam’iyya nagari domin samun shugaban kasa nagari wadda zai yi adalci ga kowa a fadin Najeriya.

Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a ranar Asabar da ta gabata a garin Dutse a shelkwatar jam’iyyar, a lokacin da ya zo yakin neman goyan bayan jama’ar Jigawa musamman masu ruwa da tsaki wajen zaban shugaban jam’iyyar da za a yi nan gaba kadan a Abuja.

Ya ce a lokacin da suka je Sokoto, mutane sun yi masu alkawarin za su zabe su sak, tun daga sama har kasa, haka jahar Katsina za su basu hadin kai dari bisa dari, yayin da jahar Kano suka yi masu alkawarin sun daure dukkan kuri’unsu sun saka a cikin buhu babu wadda za ta kauce gaba daya tasu ce, saboda haka suna neman goyan bayan jama’ar Jigawa su ma su ba su nasu kuri’un domin ganin sun kai ga biyan bukata.

“Ku tsaya ku yi bakin kokarinku wajen zaban shugaba nagari a jam’iyyarmu, shugaba nagarin shi ne wanda zai iya samar da shugaban kasa nagari wanda zai iya samar da sauyi mai ma’ana a cikin Najeriya, shugaban da zai iya dawo da martabar PDP a Najeriya, kuma babu wanda zai iya yin hakan sai Gbenga Daniel, kuma ina tabbatar maku ba zan ci amanarku ba, zan cika maku dukkan alkawuran da na dauka a gabanku,” in ji shi.

Ya kara da cewar, “Na fahimci cewa Jahar Jigawa mallakar jam’iyyar PDP ce, saboda haka nan bada wani bata lokaci ba zamu kori wadanda suke yin haya a cikin gidanmu da muka ba su haya wato gidan gwamnati. Ya bayyana gwamnan jahar Jigawa na APC shi ne dan hayar da yake haya a gidan gwamnatin jahar ta Jigawa, kuma zamu kore shi da zarar mun kafa gwamnati a 2019”

Shi ma da yake karanta jawabin maraba, shugaban jam’iyyar ta PDP na Jahar Jigawa, Alhaji Salisu Mamuda Kuit ya ce su a jahar Jigawa ‘ya’yan PDP kansu a hade ya ke, kuma dukkan kuri’unsu a hade suke babu wata kuri’a da zata kauce, ya kuma yi alkawarin cewar dukkan kuri’unsu na Gbenga Daniel ne. Sannan sai ya bukaci goyan bayan jama’ar Jahar Ogun domin marawa mai gidansu, Alhaji Sule Lamido baya akan burinsu na neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2019, ya ce hakan ba zai yiwu ba dole sai da hadin kansu.