PDP na iya lashe daukacin mukamai a zabe mai zuwa a Taraba – Mafindi

Injiniya Yahaya Mohammed Mafindi ya rike mukamai da dama da a Jihar Taraba da suka hada da har da kwamishina, yanzu shi ne mai ba Mukaddashin Gwamnan Jihar shawara a kan ilimin kimiyyar sadarwar zamani. A cikin wannan hirar ya yi magana kan halin da jam’iyyarsu ta PDP ke ciki: Kana cikin kusoshin Jam’iyyar PDP […]

PDP na iya lashe daukacin mukamai a zabe mai zuwa a Taraba – Mafindi
PDP na iya lashe daukacin mukamai a zabe mai zuwa a Taraba – Mafindi

Injiniya Yahaya Mohammed Mafindi ya rike mukamai da dama da a Jihar Taraba da suka hada da har da kwamishina, yanzu shi ne mai ba Mukaddashin Gwamnan Jihar shawara a kan ilimin kimiyyar sadarwar zamani. A cikin wannan hirar ya yi magana kan halin da jam’iyyarsu ta PDP ke ciki:

Kana cikin kusoshin Jam’iyyar PDP a Jihar Taraba me za ka ce game da rawar da jam’iyyar za ta iya takawa a zabe mai zuwa?
Kamar yadda kowa ya sani ina daya daga cikin wadanda suka kaddamar da Jam’iyyar PDP a jihar nan a 1998, kuma ina cikinta har yanzu, amma abin dake faruwa a jam’iyyar yanzu akwai wuya jam’iyyarmu ta samu nasara kamar yadda ta saba a shekarun baya. Wannan na da nasaba ne da yadda wasu wadanda suka shiga jam’iyyar jiya-jiya, amma suka mamaye komai suka hana wadanda suka sha wahala wajen tabbatar da kafuwarta a jihar da ma kasa baki daya sakat, har ma suka kore su daga cikin jam’iyyar.
Idan ka dubi yadda aka fitar da ’yan takarar mukamai a jam’iyyar ka san ba adalci kuma ba a bi tsarin jam’iyya ba, an nuna son kai ne kawai ba tare da la’akari da hakkin ’yan jam’iyya ba. Wannan lamari ya kawo korafe-korafe a cikin jam’iyya wanda ya sa wasu jiga-jiganta suka canja sheka zuwa wata jam’iyya domin ba a yi musu adalci ba. Idan aka lura daga zaben 1999 har zuwa na shekarar 2007 kusan kashi 99 na mukamai tun daga kansila har zuwa Gwamna Jam’iyyar PDP ce ke lashewa.Wannan na da nasaba ne da irin hadin kan ’yan jam’iyya a wancan lokaci, amma abin ya soma canjawa a lokacin zaben 2011 sabo rashin adalci da son kai wajen fidda ’yan takara da ya bullo a lokacin, shi ya aka samu ’yan Majalisar Wakilai da ’yan majalisun jiha daga jam’iyyar adawa.
To yanzu da yake kawunan ’yan jam’iyya sun rabu kan dalilin da ka ambata yaya kake ganin yadda zabuka za su kasance a wannan karo?
Abu ne mai wuya a ce Jam’iyyar PDP za ta lashe daukacin mukamai a lokacin zabe mai zuwa a Jihar Taraba, domin kamar yadda na fadi a can baya da yawa daga cikin ’ya’yan jam’iyya sun fusata har wasu sun canja sheka saboda rashin gamsuwa da yadda aka fidda ’yan takara a jam’iyyar. Wannan ba karamin cikas zai kawo ga jam’iyya ba, kuma har yanzu ba a dauko hanyar yin gyara ba. Ya kamata a ce jam’iyya ta nemi ’ya’yanta da suke da korafi a zauna da su a ba su hakuri kan abin da ya faru, amma an ki yin haka. Kuma mafi yawan wadanda aka saba mawa su ne tsofaffin ’yan jam’iyya da suka bauta mata shekara da shekaru. Matsala babba ita ce wasu suna nan a cikin jam’iyyar amma in ba a yi hattara ba za su yi mata illa ta hanyar zaben wata jam’iyya a lokacin zabe don huce haushinsu. Irin wadannan abubuwa ne shugabannin jam’iyya a jiha suka kasa fahimta ko kuma da gangan sun ki yi haka don wata manufa.
Akwai batun mayar da mulki zuwa Kudancin Jihar Taraba wanda shi ma yana kawo matsala ga jam’iyyar, yaya kake kallon haka?
To wannan magana mai sauki in wasu sun ce akwai yarjejeniya kamar haka sai a fada mana a ina aka yi wannan yarjejeniya, kuma su wane ne suka zauna suka kulla yarjejeniyar. In akwai bukatar haka zama ya kamata a yi cikin lumana da fahimta ta yadda za a samu yardar juna, ba wai kawai a ce da karfi da yaji za a ce dole a maida mulki wani bangaren jihar ba, wannan ba dimokuradiyya ba ne, amma in an yi tuntuba tare da zama na gaskiya kuma aka samu fahimta to haka ba laifi ne ba.
Ana kukan rashin dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyu masamman a PDP, mene ne ra’ayinka kan wannan matsala?
Gaskiya ne akwai rashin dimokuradiyya a cikin gida ba kawai a Jam’iyyar PDP ba ne har da wasu jam’iyyu.
To, amma da yake ni dan PDP ne ya kamata maganata ta tsaya ga jam’iyyar. Kowa ya san akwai matsalar rashin dimokuradiyya na cikin gida a jam’iyyarmu ta PDP musamman a halin da ake ciki. In ka lura wannan matsala ita ce ta kawo rashin jituwa a tsakanin ’yan jam’iyyar ba kawai a Jihar Taraba ba, har a jihohi da yawa a kasar nan inda wannan matsala ta haifar da rarrabuwar kawunan ’yan jam’iyya. Kuma kamar yadda na fadi in ba a yi hattara ba, ko aka dauki matakin lallashi ’yan jam’iyyar da suka yi fushi ba, to jam’iyyar za ta fuskanci koma-baya a zaben 2015.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya