PDP na son dawowa mulki ne don mai da hannun agogo baya – Gololo
Dan Majalisar Wakilai daga mazabar Gamawa a Jihar Bauchi, Alhaji Mohammed Garba Gololo ya ce PDP na hankoron sake dawowa mulki ne don mayar da hannun agogo baya. Dan majalisar ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya su yi watsi da kalaman da suke fitowa daga bakin wadansu ’yan siyasa da malaman addini da suke […]
Dan Majalisar Wakilai daga mazabar Gamawa a Jihar Bauchi, Alhaji Mohammed Garba Gololo ya ce PDP na hankoron sake dawowa mulki ne don mayar da hannun agogo baya.
Dan majalisar ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya su yi watsi da kalaman da suke fitowa daga bakin wadansu ’yan siyasa da malaman addini da suke hasashen cewa za a yi rikici a lokacin zaben bana.
Ya yi kiran ne a zantawarsa da Aminiya a Ibadan inda ya ce, “Muna fata idan Allah Ya yarda za a yi zabe mai tsabta da zai gamsar da kowa a Najeriya da duniya baki daya kamar yadda aka yi zaben 2015. Masu hasashen yiwuwar tashin hankali a wannan zabe, suna shiga kafofin labarai suna cewa za a yi tashin hankali a zabe mai zuwa suna fadin haka ne domin cimma buri na kashin kansu, amma ba burin miliyoyin jama’a ba.”
“Gwamnatin Tarayya ta riga ta dauki matakan dakile irin wadannan mutane da miyagun iri a ciki da wajen Najeriya, wadanda ake hayar su domin yin zagon kasa ga ayyukan ci gaba da wannan gwamnati take yi a ko’ina a Najeriya. Saboda haka nake yin kira ga dukan ’yan Najeriya su dawo daga rakiyar irin wadancan mutane su daina sauraron bayanan da suke yi,” inji shi.
Mohammed Gololo ya kawo misali da ayyukan tsaron kasa da gwamnati ta sa a gaba inda ya ce, “An samu tabarbarewar harkokin tsaro kafin zuwan wannan gwamnati a sashen Arewa maso Gabas a inda ’yan Boko Haram suka rike ragamar wasu kananan hukumomi suna cin karensu babu babbaka.
“Mabiya addinai sun daina shiga wuraren ibada suna tunzura jama’a, miliyoyin mutane sun tagayyara sun kaurace wa garuruwansu, saboda ta’addancin Boko Haram. Amma zuwan wannan gwamnati ta fatattake su aka samu zaman lafiya. Wannan ya isa mutane su gane babban kuskuren da gwamnatin baya ta tafka da take son dawowa domin mayar da hannun agogo baya,” inji shi.
Dangane da hayaniyar da takwarorinsa ’yan majalisa suka yi a majalisa lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin bana sai ya ce “Abin da ya auku a wannan lokaci siyasa ce kuma yana daga cikin tsarin dimokuradiyya. Idan har dukan wakilai suka kulle kansu cikin zaure suka tashi suka goyi bayan abu daya to, ina ganin ba a bai wa juna gaskiya ba, domin dole ne a samu mai so da wanda ba ya so shi ne dimokuradiya. Wanda yake ganin ya yi ihu ne domin cin mutuncin Shugaban Kasa ya ci mutuncin kansa ne.”