PDP na zawarcin Atiku

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Adamawa, Abdurrahman Bobboi ya ce jam’iyyarsu na iya kokarinta don ganin sun dawo da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar zuwa jam’iyyar. Abdurrahman Bobboi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin jam’iyyar PDP dake jahar, inda ya ce jam’iyya mai mulki ba […]

PDP na zawarcin Atiku

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Adamawa, Abdurrahman Bobboi ya ce jam’iyyarsu na iya kokarinta don ganin sun dawo da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar zuwa jam’iyyar.

Abdurrahman Bobboi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin jam’iyyar PDP dake jahar, inda ya ce jam’iyya mai mulki ba za ta iya rike Atiku ba.

“PDP na kasa da jiha baki daya na iya kokarinta don canza ra’ayin tsohon shugaban kasar da sauran wadanda suka bar jam’iyyarsu domin dawo wa jam’iyyarsu ta asali. Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kasance mai taimakawa jam’iyyar wadda ya kunshi kudi da kuma shawarwari. Kasancewarsa tsohon mataimakin shugaban kasa, ya san yadda siyasar kasar take, don haka dole ne mu yi iya kokarinmu don ganin ya dawo jam’iyyarmu”. Inji shi.

Ya kara da cewa “Duk da cewa Atiku ya kasance mutum mai basira da fasaha da kuma iya siyasa, jam’iyyar APC ba ta ba shi damar magance ma su matsalolinsu wadanda suka shafe kasar nan. Kwamitin sasantawa na jahar, tsohon gwamnan jahar, Boni Haruna zai jagorance shi sannan akwai wadansu kwamiti wadanda suka kunshi kwamitin tarbiyya da dai sauransu wadanda Goni zai jagoranta.

Bobboi ya jinjina kuma ya yi barka ga kwamitin Ahmed Makarfi wadanda aka ba su rikon kwaryar jami’iiyar a yanzu, sannan ya bukaci ‘yan Najeriya da su bada hadin kai da kuma goyon baya ga jam’iyyar PDP, don ci gaban kasar baki daya.